Gwamnatin Buhari
Gwamnatin tarayyan Najeriya ta baiwa ma'aikatan hutun ranar Litinin 29 ga Mayu domin murnar ranar rantsar da zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Buhari ya bayyana bin dokan kundin tsarin mulki na bayyana kadarorinsa kafin da kuma bayan ya shiga ofishinsa haka ne zai inganta aiki da bin ka'ida.
A jiya ne aka ji Gwamnatin tarayya ta bada sabuwar kwangilar titin N90bn daf da Bola Tinubu zai hau mulki. Aikin fadada titin Akure/Ado-Ekiti da zai ci N90bn.
Charles Soludo ya rubutawa shugaban kasa wasika a kan batun Nnmadi Kanu. Gwaman Anambra ya na so a saki Shugaban kungiyar IPOB kafin Muhammadu Buhari ya sauka
Ministan ilimi a gwamnatin Buhari Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa baya da ilimin komai a bangaren ilimi lokacin da shugaban kasa ya ba shi mukamin ministan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a nada sabon shugaba a hukumar NACETEM da ke Ile Ife. Wa'adin Darekta Janar na hukumar NACETEM ya fara aiki tun 13 ga Mayu.
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi ikirarin cewa masu cin hancu a fadar shugaban kasa kuma su ne suka ƙulla masa makircin faduwa zaben Sanata a 2023.
Za a ji Shugaban kasa ya amince da kwangiloli domin gyara wutar lantarki a Daura. Gwamnatin tarayya ta yarda ayi ayyukan wuta a jihohin Katsina, Yobe da Ogun.
Majalisar zartarwa tayi zaman da ya kasance na ban-kwana. A nan ne Ministoci su ka fito karara su ka fadawa Shugaban kasa abin da suke ganin shi ne daidai.
Gwamnatin Buhari
Samu kari