Ministoci Sun Ci Gyaran Shugaban Kasa, Sun Zargi Buhari da Sabawa Kundin Tsarin Mulki

Ministoci Sun Ci Gyaran Shugaban Kasa, Sun Zargi Buhari da Sabawa Kundin Tsarin Mulki

  • Ministoci sun yi zama na karshe da Muhammadu Buhari a taron FEC da aka yi a ranar Laraba
  • Wasu Ministoci sun fadawa shugaban kasa doka ba ta san da zaman kujerarsu ta karamar Minista ba
  • Festus Keyamo ya na da wannan ra’ayi, ya ce babu dalilin Minista ya zama karkashin wani Ministan

Abuja - Wasu Ministoci biyu da za su bar ofis sun fito sun yi ikirarin kundin tsarin mulkin Najeriya bai san da zaman wata kujerar karamar Minista ba.

Festus Keyamo SAN da Ramatu Tijjani Aliyu wadanda suke rike da mukaman kananan Minista suka fadi haka, Premium Times ta kawo rahoton.

Karamin Ministan kwadago na kasar ya shaidawa Shugaban kasa mai barin-gado cewa kujerar da suke rike da ita, ta ci karo da kundin tsarin mulki.

Wasu Ministoci
Wasu Ministoci a FEC Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

A jawabin karshe da ya yi a taron FEC, Festus Keyamo SAN ya ce tsarin da ake tafiya na hada Ministoci biyu a ma’aikatar tarayya guda bai aiki da kyau.

Kara karanta wannan

Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da kujerun Ministoci ba su da yawa kuma ya zama dole a nada Minista daga kowace Jiha, shugabannin Najeriya sun kirkiro karamin Minista.

Da yake jawabi a jiya, an rahoto Keyamo ya na cewa sashe na 147 na kundin tsarin mulki da ya kafa ofishin Ministan tarayya bai bambance kujerar ba.

Keyamo da Ramatu Aliyu sun koka

Ministan mai barin-gado ya ce babu bambanci wajen rantsuwa tsakanin Minista da karamin Minista, ya ce hakan tamkar a kirkiro wani sabon ofis ne.

Jaridar ta ce wannan shi ne korafin karamar Ministar harkokin birnin tarayya watau Ramatu Tijjani Aliyu, ta ce hakan ya rage masu karfi a majalisar FEC.

Duk da Ministocin gwamnatin nan sun samu damar yin aikinsu yadda ya kamata, Ramatu Aliyu ta ce maida wasu kananan Ministoci ya jawo tawaya.

Kara karanta wannan

Gyaran Hali: Kotu Ta Umarci a Zane Wani Matashi Barawon Kaji Da Ransu Bulali 8 a Kaduna

Mai girma Ministar ta na ganin babu adalci a irin tsarin da ake tafiya a yanzu, duk da ta godewa gwamnati a kan damar da ta samu na yi wa kasarta aiki.

Shawarar da Keyamo ya bada shi ne a barka ma’aikatun ta yadda Minista zai zama karkashin shugaban kasa kai-tsaye a maimakon wani abokin aikinsa.

An kai Gwamnati kotu

Rahoto ya zo cewa ana karar Shugaban Najeriya da wasu Ministocinsa da kuma ofishin kula da bashi (DMO) na kasa a dalilin shirin karbo aron $800m.

Patrick Osagie Eholor zai yi shari’a da bankin Duniya da kungiyoyin cigaban kasashen waje a kotun tarayya da ke Asaba kan batun bashin da ake nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng