Jihar Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Mutawali Shettima Bukar a matsayin sabon Wazirin Borno. Shehun Borno, Abubakar Elakanrmi ya mika sunan Bukar.
Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya umurci dukkanin ciyamomin kananan hukumomin jihar da su rinka sa hannu a na'urar shaidar zuwa aiki sau hudu a rana.
Zagazola Makama ya tabbatar da cewa wani abun fashewa da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa ya yi ajalin akalla manoma 7 tare da jikkata wasu a jihar Borno.
Gwamna Babagana Umaru Zulum ya ce matuƙar yan Najeriya na son ƙasar nan ta matsa daga inda take sai sun rika bin doka da ka'iddan a kowane abu suke yi.
Wani bam da ya tashi a jihar Borno ya yi sanadiyyar rasuwar wasu mutum shida. Bam din ya tashi ne a karamar hukumar Gubio ta jihar a ranar Asabar.
A cikin jihohin Najeriya 36 da ake da su, akwai wadanda suka fi sauran yawan fadin kasa. Daga ciki mun tattaro muku jihohi 13 wadanda suka fi yawan fadin kasa.
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa Boko Haram ta lalata gidaje sama da kaos 90 a jihar Borno amma zuwa yanzu sun fara kokarin sake gina gidajen.
Kungiyoyin 'yan ta'adda na ISWAP da na Boko Haram sun yi wani kazamin fada a tsakaninsu, wanda ya yi silar mutuwar mutane da dama a Tafkin Chadi.
A koƙarin kwato wuraren da ke hannun ƴan ta'adda a jihar Borno, sojoji da sauran jami'an tsaro sun faɗa tarkon mayakan Boko Haram, an rasa rayukan jami'an tsaro 3.
Jihar Borno
Samu kari