"Yan Ta'adda Sun Lalata Kaso 90 Cikin 100 Na Gidajen Al'ummar Jihata" Gwamna Ya Faɗi Gaskiya

"Yan Ta'adda Sun Lalata Kaso 90 Cikin 100 Na Gidajen Al'ummar Jihata" Gwamna Ya Faɗi Gaskiya

  • Farfesa Zulum ya ce tun daga farkon ɓullar ƙungiyar Boko Haram zuwa yanzu ta lalata kaso 90 cikin 100 a gudajen al'ummar jihar Borno
  • Gwamnan ya bayyana cewa a shekaru 12 da suka wuce, gwamnatinsa da waɗanda suka gabace shi sun yi kokarin sake gina gidajen
  • Ya ce a yanzu zai haɗa kai da wasu ƙungiyoyi domin cike giɓin da ke akwai domin maida ƴan gudun hijira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya bayyana cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun lalata sama da kashi 90 cikin 100 na gidaje a jihar.

Amma Zulum ya ce babban abin farin cikin shi ne gwamnan da ya gabace shi da kuma shi kansa sun sake gina sama da kaso 30-40 na gidajen da ƴan ta'addan suka lalata a shekara 12 da suka wuce.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa

Gwamna Babagana Zulum.
Boko Haram sun lalata sama da kashi 90 na gidaje a Borno – Zulum Hoto: Prof. Babagana Umaru Zulum
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce duk da kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen sake gina wuraren da aka lalata, har yanzu jihar na da babban gibi wanda bai gaza na gidaje 500,000 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, a wajen bikin bayar da lambar yabo ta samar da gidaje na kungiyar IOM a Abuja, The Nation ta ruwaito.

"Zamu ƙara gida gidaje mu maida ƴan gudun hijira"

A ruwayar Channels tv, Gwamna Zulum ya ce:

"Gwamnatin jihar Borno da shiyyar Arewa maso Gabas za su samar da duk abin da ake buƙata a siyasance domin haɗin guiwa da IOM da sauran ƙungiyoyi wajen gina wa ƴan gudun hijira gidaje.
"Nan bada daɗewa ba zamu ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar IOM domin ganin yadda zamu haɗa kai mu gina ƙarin gidaje. Yanayin tsaron jihar Borno ya inganta da ƙaso 90, muna iya bakin kokarinmu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

"Muna da wurare da yawa masu tsaro don haka za mu yi duk mai yiwuwa don ganin an gina gidaje tare da maida mutane cikin mutunci, kamar yadda babban taron Kampala ya nuna."

Dangane da gibin gidajen da ke akwai a Borno, Gwamna Zulum ya ce daga ɓullar Boko Haram zuwa yau, "ƴan ta"addan sun lalata kaso 90 na gidajen Borno."

Ya ƙara da cewa, "A cikin shekaru 12 da suka gabata, kama daga gwamnan da ya gabata zuwa yau, ina ganin mun gina sama da kashi 30-40 amma har yanzu muna da gibi mai dimbin yawa, wanda bai gaza gidaje 500,000 ba.”

An kashe masu garkuwa 3 a Adamawa

A wani rahoton na daban Tsagerun masu garkuwa da mutane 3 sun bakunci ƙahira yayin musayar wuta da ƴan sanda a jihar Adamawa.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce dakarun sun ceto mutum 3 da maharan suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel