'Yan Ta'adda Sun Yi Wa Sojoji Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Rayuka Tare da Tafka Mummunar Ɓarna

'Yan Ta'adda Sun Yi Wa Sojoji Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Rayuka Tare da Tafka Mummunar Ɓarna

  • Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mamayi dakarun sojin Najeriya, sun buɗe musu wuta a jihar Borno
  • Wata majiya daga cikin sojojin ta ce ƴan ta'addan sun kashe soja ɗaya da wasu jami'an tsaro biyu a harin
  • Ya ce bisa tilas sojoji da sauran jami'an tsaro suka ja da baya saboda karfin luguden wutan mayakan Boko Haram

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe wani Laftanar na Soji da wasu ‘yan banga biyu a wani harin kwantan bauna da suka kai yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno.

Duk wani yunkuri na jin bakin rundunar sojin Najeriya kan wannan hari da ƴan ta'addan suka kai kan sojoji ranar Asabar ya faskara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Yan ta'adda sun farmaki dakarun soji a Borno.
Boko Haram Sun Kai Faramaki Kan Sojoji a Jihar Borno, Sun Kashe Rayuka Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ta wayar salula bai ɗaga kiran ba kuma bai amsa sakonni ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan ta'adda suka yi wa sojoji kwantan ɓauna

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa an kai harin ne bayan sojoji sun karbe yankin Krenowa da ke karamar hukumar Marte, kwanaki biyar da suka gabata.

Kwace sansanin ƴan ta'addan da sojoji suka yi wani ɓangare ne an yunƙurin rundunar tsaron Najeriya na faɗaɗa yaƙi da ta'addanci a shiyyar.

Sai dai wata majiya ta ce:

"Dakarun sojin na rundunar 50 Task Force Brigade sun faɗa tarkon bama-bamai wanda suka fara tashi da su a Krenowa, lamarin da ya tilasta musu janyewa, suka jefar da babura 12 cikin 15 na aikin."

Ya ce sojojin da yawansu ya haura dari kuma dauke da manyan motocin yaki da sauran kayan aiki sun koma garin Marte.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji yan ta'adda sun ceto mutanen da suka sace a Kebbi

Wani soja ya ce wata tankar yaƙi ta sulke (APC) ta lalace a harin wanda ya faru da misalin karfe 1 na safe yayin da direban ya tsere da rauni a kafa.

Ya ce:

"Mun kai samame har maɓoyar ƴan ta'adda amma kwatsam muka tsinci kanmu a cikin ruwan wuta wanda ya tilasta mana janye wa. Ina da yaƙinin ɓuya suka yi saboda babu alamun ko mutum ɗaya.
"Mun koma mun samu mafaka a sansanin rundunar 27 Task Force da ke garin Marte."

Ya ce ba a samu damar ɗauko gawarwakin soja ɗaya, mamban jami'an sa'kai JTF da ɗan banga guda ɗaya ba nan take saboda karfin luguden wutan ƴan ta'addan, rahoton Nairaland.

An ci gaba da kashe-kashen rayuka a Filato

A wani rahoton kun ji cewa Ƴan ta'adda sun ci gaba da kashe bayin Allah a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato duk da sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24.

Rahoto ya nuna cewa mutanen da ba su gaza 30 ba sun rasa rayuwarsu yayin da ƴan bindiga suka shiga wani kauye da safiyar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel