Gwamnan Arewa Ya Cire Tsoro, Ya Faɗi Abu 1 da Ƴan Najeriya Zasu Yi Su Samu Sauƙi da Ci Gaba

Gwamnan Arewa Ya Cire Tsoro, Ya Faɗi Abu 1 da Ƴan Najeriya Zasu Yi Su Samu Sauƙi da Ci Gaba

  • Gwamna Zulum ya bayyana muhimmin abun da ya hana Najeriya ci gaba wanda a cewarsa sai kowane ɗan ƙasa ya canza kansa
  • Babagana Zulum ya ce idan har ana son samun ci gaba a ƙasar na ya zama dole ƴan Najeriya su riƙa bi doka da ƙa'idoji
  • Ya kuma yi magana kan batun cin hanci da rashawa da kuma yanayin tsaro a jihar Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ce Najeriya ba zata taɓa samun ci gaba ba matuƙar ƴan kasa ba su bin doka da oda.

Zulum ya yi wannan furucin ne a wajen rufe taron lakcar tunawa da Sir Ahmadu Bello karo na 10 wanda aka yi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da amarya da ƙawayenta suka mutu jim kaɗan bayan ɗaura aure a arewa

Gwamma Babagana Umaru Zulum.
Zulum: Dole ne mu bi dokoki da ka’idoji domin Nijeriya ta samu ci gaba Hoto: Prof. Babagana Umaru Zulum
Asali: Twitter

The Cable ta tattaro Zulum na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Najeriya shi ne rashin bin dokoki da ka’idoji. Ba za mu taɓa ganin daidai a al'amuran mu ba har sai mun bi doka da ƙa'idoji."

Gwamnan ya kuma lura cewa kasar nan ba za ta daidaita ba idan har cin hanci da rashawa ya ci gaba da yaduwa.

Farfesa Zulum ya kara da cewa ya zama wajibi shugabanni da mabiyansu "su haɗu wuri guda wajen bin dokoki da ka'idoji a harkokinsu na yau da kullum."

Mun shawo kan matsalar tsaron Borno - Zulum

Ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin samar da shugabanci na gari ta hanyar mai da hankali kan tsaro, aiwatar da muhimman ayyuka, cika alkawuran kamfe, da kara wa ‘yan kasa karfin gwiwa.

Kara karanta wannan

Babban minista ya fadi abu 1 da yake hana Shugaba Tinubu barci

Gwamnan ya ci gaba da cewa:

"Wadannan ci gaban sun nuna nasarorin da muka samu ta hanyar shugabanci nagari da kuma ganar da al'umma irin hanyoyin da muka biyo domon kawar da ƴan bindiga da ƴan tada kayar baya.”
"Mun samu saukin matsalar tsaro a Borno da kaso 95 cikin ɗari kuma idan Allah ya so kafin ƙarewar wa'adin gwamnatina, Borno zata fita daga matsalar ƴan tada ƙayar baya."

Shettima ya gano matsalar arewa

A wani rahoton na daban Sanata Kashim Shettima ya bayyana muhimmin abinda ya haifar da ayyukan ta'addancin ƴan bindiga a Arewacin Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya ce cin hancin da ya yi wa shugabanni katutu, shi ne tushen matsalar tsaron da ta addabi arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262