Hadarin jirgi
Da safiyar yau ce Juma'a 1 ga watan Disamba jirgin saman sojin Najeriya ya yi hatsari inda jirgin ya tarwatse a birnin Port Harcourt da ke jihar Ribas.
Bayan kwashe shekaru 80 ana nema, rahotanni sun bayyana cewa an gano jirgin yakin da ya bace tun a lokacin Yakin Duniya na biyu. Warren Singer ne matukin jirgin.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da mutuwar wani jami'inta yayin wani mummunana hatsarin jirgin ruwa da ya kife a tsakiyar ruwa a jihar Ribas a ranar Asabar.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da cewa fasinjoji 10 sun kwanta dama a wani sabon haɗarin kwale-kwale da ya afku a Shiroro ta jihar Neja.
Wani jirgin sama na kamfanin ValueJet ya gamu da hatsari a filin jirgin sama na Port Harcourt a jihar Rivers. Jirgin na ɗauke da fasinjoji 67 da ma'aikata biyar.
An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a birnin Abuja sakamakon matsalar da aka samu a lokacin da wani jirgi ya sauka amma bai samu ta sauki ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an ƙara samun hatsarin jirgin ruwa a jihar Nasarawa, karo na 16 kenan jumulla a baya-bayan nan kuma mutum huɗu sun rasu.
Ministan wutar lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabi, ya share tababa kan halin da yake ciki bayan hatsarin jirgin saman da ya ritsa da shi a Ibadan jiya Jumu'a.
Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin sama ya gamu da matsala a filin sauka da tashin jiragen sama da ke Ibadan, babban birrnin jihar Oyo ranar Jumu'a daddare.
Hadarin jirgi
Samu kari