Mutane Sama da 20 Sun Mutu Yayin da Jirage Biyu Suka Yi Mummunan Hatsari a Jihar PDP

Mutane Sama da 20 Sun Mutu Yayin da Jirage Biyu Suka Yi Mummunan Hatsari a Jihar PDP

  • Wasu jiragen ruwa guda biyu sun gamu da mummunan hatsari a yankin ƙaramar hukumar Andoni ta jihar Ribas jiya Talata
  • Shugaban ƙaramar hukumar Andoni ya ce akalla mutane 20 suka mutu a haɗarin, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa
  • Mista Awartu ya kuma nuna kaɗuwa da takaicinsa bisa faruwar ibtila'in, inda ya yi alƙawarin agazawa waɗanda ya shafa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Akalla mutane 20 ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a magudanar ruwa ta Andoni da ke karamar hukumar Andoni a jihar Ribas.

Wannan mummunan lamarin wanda ya auku ranar Talata da daddare, ya rutsa da jiragen ruwa guda biyu na haya waɗanda suka nufi garin Bonny, mai makoftaka da gabar tekun.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori dukkan kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa a arewa, ya faɗi dalili

Hadarin jirgin ruwa.
Mutane 20 sun mutu a wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a jihar Rivers Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

Shugaban ƙaramar hukumar Andoni, Erastus Awortu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rattaba wa hannu da safiyar Laraba, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Awartu ya nuna matuƙar kaɗuwarsa bisa wannan mummunar kaddara da ta afku, kana ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan da sauran al'ummar yankin.

Ciyaman ɗin ya bayyana takaicin cewa hatsarin ya faru ne bayan an yi nasarar gudanar da shagulgulan bikin al'ada ciki har da bikin hadin kai a yankin ƙaramar hukumar.

Gwamnati zata taimaka iyalan mamatan

Ya kuma yi bayanin cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen ceto wadanda suke raye, ba da agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata da tsamo gawarwakin wadanda suka mutu daga kogin.

Ya kuma ɗauki alkawarin cewa zasu yi kokarin rage raɗaɗin iyalan waɗanda suka mutu da sauran al'umma a irin wannan lokaci mara daɗi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a garuruwa 3, sun kashe rayuka da yawa a arewa

Bugu da kari, ya jaddada bukatar cewa masu kwale-kwale su bi duk hanyoyin da ya dace domin kare lafiyar fasinjoji, kana ya basu shawarar gujewa tafiye-tafiyen cikin teku da dare.

A rahoton Daily Trust, Awartu ya ce:

"Muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, musamman mazauna Garin Ngo, Ataba, Isiama, da sauran kauyukan da haɗarin ya rutsa da ‘yan uwansu.
"A matakin gwamnatin ƙaramar hukuma, za mu yi duk abin da za mu iya don rage radadin dangogi da al’ummar da suka rasa ƴan uwansu."

Yan bindiga sun kai sabon hari a Benue

A wani rahoton kun ji cewa Yan bindiga sun kai sabon mummunan hari kauyuka uku a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benuwai ranar Lahadi.

Rahoto ya nuna cewa maharan waɗanda ake zargin fulani ne sun halaka mutane bakwai a hare-haren da suka kai lokuta daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262