Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari Tare da Tarwatsewa da Safiyar Yau, Bayanai Sun Fito

Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari Tare da Tarwatsewa da Safiyar Yau, Bayanai Sun Fito

  • Mummunan hatsarin jrgin sama ya faru da safiyar yau Juma’a a birnin Port Harcourt da ke jihar Ribas
  • Lamarin ya faru ne a yau Juma’a 1 ga watan Disamba a birnin Port Harcourt da ke jihar wanda ya yi sanadin tarwatsewar jigin
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru da safiyar yau inda har yanzu ba a tabbatar da mutane nawa su ka mutu ba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ribar – Jirgin yakin sojin sama a Najeriya ya fadi a tare da fashewa a sansanin sojin sama da ke Port Harcourt a jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne a yau Juma’a 1 ga watan Disamba a birnin Port Harcourt da ke jihar wanda ya yi sanadin tarwatsewar jigin.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun halaka dan bindiga, sun ceto malamin addini da wasu mutum 2 a jihar arewa

Jirgin yakin saman Najeriya ya yi hatsari a Ribas
Hatsarin jirgi ya rusa da jirgin saman sojin Najeriya. Hoto: NAF.
Asali: Facebook

Mene ya jawo hatsarin jirgin sama?

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu ainihin dalilin da ya jawo faduwar jirgin ba, cewar BBC News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Punch ya tabbatar da cewa hatsarin jirgin sojin sama ya fadi ne da misalin karfe 7:50 na safe.

Wata majiya tace:

“Ina cikin daki na ji karar fashewar jirgin da safiyar yau Juma’a a sansanin sojin saman da ke birnin Port Harcourt.
“Abin da na gani kawai shi ne bakin hayaki ya turnuke sama, sai dai ban san ko akwai wadanda su ka mutu ba saboda ba zan iya zuwa wurin ba.”

Wane martani sojin sama su ka yi?

Kakakin rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma'a 1 ga watan Disamba.

Gabkwet ya ce dukkan wadanda ke cikin jirgin sun tsira da rayukansu sai dai sun samu raunuka, cewar Arise News.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addinin musulunci da amarya da ango a Kaduna

Ta ce:

"Abin farin ciki shi ne dukkan wadanda ke cikin jirgin su biyar sun tsira da rayukansu sai dai sun samu raunuka.
"Tuni aka kwashe su zuwa asibitin sansanin sojin sama da ke Port Harcourt don ba su kulawa.
"Hafsan sojin saman kasar, Hassan Abubakar yanzu haka ya na kan hanyar zuwa Port Harcourt don gani da idonsa."

Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin wani soja

A wani labarin, wani mummunan hatsarin jirgin ruwa ya hallaka wani soja a jihar Ribas.

Hatsarin ya faru ne a karshen makon da ya gabata bayan igiyar ruwa ta yi jifa da jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel