Jimami Yayin da Jarumin Soja Ya Rasa Ransa a Wani Mummunan Hatsarin Jirgin Ruwa da Ya Kife

Jimami Yayin da Jarumin Soja Ya Rasa Ransa a Wani Mummunan Hatsarin Jirgin Ruwa da Ya Kife

  • Mummunar hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin wani jarumin soja yayin da su ke bakin aiki don kare martabar kasa a jihar Ribas
  • Marigayin ya gamu da tsautsayin ne yayin da su ke tsaka da tafiya a kogin Bolo da karamar hukumar Ogu/Bolo a jihar
  • Mataimakin daratan yada labarai na rundunar da ke shiyya ta 6, Manjo Jonah Danjuma shi ya tabbatar da haka

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ribas – Rundunar sojin Najeriya shiyya ta 6 da ke Port Harcourt a jihar Ribas ta tabbatar da mutuwar jami’inta a hatsarin jirgin ruwa.

Rundunar ta ce jami’in nata ya rasa ransa ne a karshen wannan mako da ya wuce a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Kano: Mahaifiyar wani rikakken dan daba ta mika shi hannun yan sanda

Sojan Najeriya ya rasa ransa yayin wani mummunan hatsarin jirgin ruwa
Sojan ya mutu a ranar Asabar da ta gabata. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Mene dalilin hatsarin jirgin ruwan?

Vanguard ta tattaro cewa sojan da ke bakin aiki ya gamu da tsautsayin ne a kogin Bolo da ke karamar hukumar Ogu/Bolo da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hatsarin jirgin ruwan ya kife ne yayin da su ke tsaka da tafiya a kan ruwa inda sojan daya tilo ya rasa ransa.

Mataimakin daratan yada labarai na rundunar da ke shiyya ta 6, Manjo Jonah Danjuma shi ya tabbatar da haka.

Ya ce jirgin ruwan da ke dauke da sojan ya kife bayan cin karo da igiyar ruwa inda nan take aka rasa shi kafin daga bisani a tsinci gawarshi.

Mene martanin soji kan hatsarin?

Ya ce:

“Hedikwatar rundunar sojoji ta shiyya ta 6 na alhinin mutuwar daya daga cikin jami’anta dalilin hatsarin jirgin ruwa a kogin Bolo a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kano, Bello, ya bayyana abu 1 tak da ke sa shi farin ciki a rayuwarsa

“Jirgin ruwan da ke dauke da sojan ya ci karo da mummunar igiyar ruwa ne inda ya kifar da kwale-kwalen da sojan ya rasa ransa.”

Danjuma ya kara da cewa marigayin ya sadaukar da rayuwarshi yayin kare martabar kasarshi, cewar Daily Post.

Ya ce tabbas rundunar za ta yi kewar jarumin sojan da ya rasa ransa yayin yi wa kasarshi ta gado hidima.

Mutum 1 ya rasu a hatsarin jirgin ruwa

Kun ji cewa, wani yaro ya rasu yayin da wasu su ka bace yayin hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja.

Hatsarin ya faru ne a karamar hukumar Katcha bayan jirgin ruwan ya kama da wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel