Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji 67 Ya Yi Hatsari a Rivers

Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji 67 Ya Yi Hatsari a Rivers

  • Wani jirgin sama mallakar kamfanin jiragen sama na Najeriya, ValueJet, ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin sama na Port Harcourt a jihar Rivers
  • Legit.ng ta tattaro cewa jirgin ya kauce hanyar da ta dace da shi da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba
  • Hatsarin ya faru ne kwanaki biyu kacal bayan faruwar irin wannan hatsarin a filin jirgin saman Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Wani jirgin sama na Bombardier ValueJet CRJ 900 ya zame daga titin jirgin sama a filin jirgin sama na Port-Harcourt a ranar Talata, 14 ga Nuwamba.

Legit.ng ta fahimci cewa, lamarin ya haifar da firgici na ɗan lokaci a tsakanin fasinjojin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar Gwamnatin jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna tare da sace mutane

Jirgin ValueJet ya yi hatsari a Port Harcourt
Fasinjoji da ma'aikatan jirgin sun tsira Hoto: @flyvaluejet
Asali: Twitter

ValueJet: fasinjoji, ma'aikatan jirgin sun tsira

Jirgin wanda ya sauka da misalin ƙarfe 3.32 na rana ɗauke da fasinjoji 62 da ma'aikatan jirgin biyar ya sauka daga kan hanyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, duk da abin da ya faru mai ban tsoro, jirgin mai rajista 5N-BXR ya sauka lafiya.

Vanguard ta ruwaito cewa, lamarin bai haifar da wata ɓarna ba ga jirgin.

Manajan darakta (MD) na kamfanin jiragen sama na ValueJet, Captain Dapo Majekodunmi ya bayyana cewa Captain Stanley Balami ya ruwaito cewa an samu zamewar ne saboda wani abu mai santsi a kan hanya.

Abun mai santsi dai ya sanya jirgin ya kauce hanyar da ya ke a kai.

Kyaftin Majekodunmi ya bayyana cewa ayyukan kamfanin na cigaba kamar yadda aka saba ba tare da wata matsala ba.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wata sanarwa daga hukumar gudanarwar ValueJet na cewa:

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bai wa asibiti gudunmawar naira miliyan 20, ya bayyana dalili

"Jirgin CRJ 900 Bombardier mai lamba 5N-BXR ya sauka lafiya tare da fasinjoji suna mamakin abin da zai iya faruwa saboda jirgin ya sauka lafiya ba tare da matsala ba."
"Wannan ƙaramin lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana a filin jirgin sama na Port-Harcourt."
"Kyaftin Stanley Balami ya ruwaito cewa jirgin ya gamu da zamewa saboda wani abu mai santsi a kan hanya wanda ya sa ya kasa tafiya a layin tsakiya."
"ValueJet ya kasance jirgin sama mai aminci kuma duk ayyukan kamfanin jirgin saman na yau da kullum na gudana ba tare da matsala ba."

Ministan Tinubu Ya Yi Hatsari a Jirgi

A wani labarin kuma, ministan Shugaba Tinubu ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin jirgin sama da ya ritsa da shi a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Adelabu ministan wutar lantarki na cikin jirgin saman da ya kauce wa hanya yayin da ya zo sauka a filin jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel