Jirgin sama ɗauke da Ministan Shugaba Tinubu ya yi hatsari yayin sauka a Ibadan, an samu matsala

Jirgin sama ɗauke da Ministan Shugaba Tinubu ya yi hatsari yayin sauka a Ibadan, an samu matsala

  • Wani jirgin sama da ya taso daga Abuja ɗauke da Ministan Bola Tinubu ya gamu da hatsari yayin sauka a filin jirgin saman Ibadan
  • Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya samu tangarɗa, ya sauka nesa da titinsa a cikin wani rami mai ciyayi
  • Har kawo yanzu ba a san wane halin ministan da sauran fasinjojin jirgin ke ciki ba amma jami'an agaji sun nufi wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ibadan, jihar Oyo - Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin sama mai zaman kansa ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman Ibadan da ke Alakia a jihar Oyo.

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Jirgin saman wanda ya ɗauko fasinjoji ciki har da Ministan Bola Tinubu, ya kauce wa hanya yayin sauka a filin jirgin.

Jirgin sama ɗauke da minista ya yi hatsari.
Jirgin Sama Ya Sauka Daga Kan Titinsa a Filin Jirgin Ibadan, An Samu Babbar Matsala Hoto: Adebayo Adelubu
Asali: UGC

A rahoton jaridar Daily Trust, jirgin da ke dauke da Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi hatsari a kusa da filin jirgin sama na Ibadan a jihar Oyo yayin sauka.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

An tattaro cewa wannan lamarin ya faru ne da daren ranar Jumu'a (Jiya) 3 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton ba bu cikakken bayani kan abin da ya faru da waɗanda lamarin ya shafa.

Amma da aka tuntubi babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Yemi Akinyinka, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar ta wayar tarho.

Mista Akinyinka ya bayyana cewa:

"Eh da gaske ne an samu wannan matsala, jami'an mu suna kan hanyar zuwa kai ɗauki wurin amma ba ni da cikakken bayani a yanzu. Za mu yi bayani nan gaba."

Shin fasinjoji sun ji raunuka?

Har yanzun babu wanda ya tabbatar da cewa ministan ko sauran fasinjojin da suka biyo jirgin sun samu raunuka a lamarin. Jirgin ya taso ne daga Abuja zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

Mutum 11 sun rasu wasu 11 sun samu raunika a wani kazamin hatsarin mota a jihar Kebbi

Wata majiya ta shaida cewa jirgin ya sauka nesa da inda ya dace da nisan mita 50 sannan ya kutsa cikin wani rami mai cike da ciyayi da ke kusa da titin jirgin.

Wannan haɗari na zuwa ne bayan hukumar kula da zirga-zirgan jiragen sama ta ƙasa (NiMET) ta gargadi kamfanonin jiragen sama da matuƙa jirgi su yi la'akari da yanayin hazo.

Mun kusa shafe babin ƴan bindiga - DHQ

Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ragowar kwanakin da suka rage wa ƴan ta'adda a duniya ba su da yawa kuma a kididdige suke.

Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce sojoji sun tura yan bindiga 67 barzahu sun kama 170 a makon jiya kaɗai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel