Abun Al Ajabi
Wata kotu a Yola, jihar Adamawa ta garkame wani direba David Donald a gidan yari bisa zargin ya damfari wata mata sama da bokiti biyar na giyar 'burkutu'.
Wata matar aure ta shiga rudani da damuwa bayan mijinta ya ki cewa komai duk da ya kamata tana cin amanarsa. Ya kamata ne tun a watan Oktoban 2023.
Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, ta shawarci mata akan su wanzar da zaman lafiya a gidajensu, ko da a lokacin da fada ya kaure tsakaninsu da mazajensu.
Yayin da ake fama da tsadar rayuwa da na kayan abinci, mutane a babban birnin tarayya Abuja sun hakura da cin nama inda suka koma siyan awara suna daurawa a abinci.
An tsare wasu manyan jami'ai biyu na kamfanin Binance a Najeriya, a cewar Financial Times (FT), wata kafar yada labaran kasuwanci da ke Birtaniya.
Jami'an 'yan sanda a jihar Abia sun kama wani tsoho mai shekaru 70, Marcel Udeh, kan zargin kashe 'dansa saboda ya cinye abincin da ya rage masa a tukunya.
Bayan shafe tsawon shekaru 13 a banki, wata mata ta ajiye aikinta sannan ta koma ga noma. Ta mayar da gidanta wajen kiwon kifi da kaji kuma tana samu sosai.
Wata amarya ta cika da bakin ciki yayin da ta samu labarin mai hoton da ta fi son aikinsa ba zai samu zuwa daukar hotunan bikinta ba. Mai hoton ya turo wani daban.
Wata matashiyar budurwa ta sharbi kuka saboda saurayinta ya rabu da ita sannan ya auri wata daban. Ta ce tsawon shekaru biyar suka shafe suna soyayya da mutumin.
Abun Al Ajabi
Samu kari