Abuja
Dan Majalisar Wakilan Tarayya, Hon. Garba Muhammed ya koka kan barazanar da ya ce ana masu da rayuwa, ya ce yan ta'addada da masu zanga-zanga sun yi barazana.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci ministoci su rika gayawa shugabannin kasa gaskiya komai dacinta. Ya ce ya kamata su daina kwarzanta su.
Mai martaba Muhammadu Sanusi II zai jagoranci taron Oxford Global Think Tank da za a yi a Abuja. Zai yi hadaka da wanda ya kafa bankin tanbic IBTC, Atedo Peterside.
Kwamitin majalisar tarayya kan gyaran kundin tsarin mulki a Najeriya ya amince da kafa sabuwar jiha a yankin Kudu maso Gabas, domin cika zuwa jihohi shida.
Tsohon babban jami’in soja, Manjo Janar Anthony Atolagbe (mai ritaya), ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa sauye-sauyen da ya yi a rundunonin tsaron kasar.
Ministan birnin tarayyar Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai bayyana a kotu kan shari’ar shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ba saboda kawai sunansa ya fito a jarida.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce shi ba mai magana ne da yawun Shugaba Bola Tinubu ba, duk da yana bayyana ayyukansa a matsayin jagora a birnin.
Shugabannin SDP na jihohi sun goti bayan korar tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, Shehu Gabam da wasu jiga-jigai biyu, sun ce gaskiya ta yi nasara kan mugunta.
Hukumar CDCFIB ta kori jami’an shige da fice 11, ta ladabtar da wasu 21 saboda cin hanci, karya doka da rashin ladabi, inda ta kuma ja kunne sauran jami'an NIS.
Abuja
Samu kari