Sallah: Kungiyar CAN Ta Tura Sako Mai Kama Hankali Ga Al'ummar Musulmai a Najeriya

Sallah: Kungiyar CAN Ta Tura Sako Mai Kama Hankali Ga Al'ummar Musulmai a Najeriya

  • Yayin da al'ummar Musulmai ke bikin salla karama a Najeriya, kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta yi martani
  • Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a sakon taya murna ga al'ummar Musulmai yayin da suka kammala azumi Ramadan
  • Okoh ya bukaci al'ummar Musulmai da su yi amfani da darussan da suka koya a azumi domin tabbatar da zaman lafiya a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta taya al'ummar Musulmai murnan bikin karamar sallah.

Kungiyar ta bukaci Musulmai da su yi amfani da darasin da suka koya domin tabbatar da koyar da zaman lafiya da fahimtar juna a kasar.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya aika sako, ya taya Kanawa murnar kammala azumin Ramadan

Kungiyar CAN ta taya Musulmi murnan bikin salla
Kungiyar Kiristoci ta CAN ta taya al'ummar Musulmai murnan bikin salla a Najeriya. Hoto: Muhammad Sa'ad Abubakar, Christian Association of Nigeria, CAN.
Asali: Facebook

Wane sako CAN ta tura ga Musulmai?

Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya bayyana haka a shafin Facebook a yau Laraba 19 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okoh ya ce wannan biki na da matukar muhimmanci ba iya Musulmai kadai ba har ma da dukkan kasar baki daya.

CAN ta ce duk da matsalol daban-daban da kasar ke fuskanta, ya kamata ayi amfani da wannan bukukuwa wurin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Shawarar da CAN ta ba Musulmai

"Darussan da muka koya a wannan wata ya na da tasirin wurin neman zaman lafiya da ci gaba a Najeriya."
"Yayin da muka ga karshen azumin watan Ramadan, ya kamata mu tuna cewa lokaci ne na tausayi da yafiya da kuma kawo karshen bambance-bambance a tsakanin addinai guda biyu."
"Muna taya al'ummar Musulmai murnan kammala azumin watan Ramadan lafiya da kuma bukukuwan sallah karama."

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

- Daniel Okoh

Okoh ya bukaci shugabanni da su inganta rayuwar 'yan ƙasar inda ya ce dole shugabanci sai da gaskiya da kuma tausayawa.

An bankado shirin wargaza Kano

A baya, mun kawo muku labarin cewa rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta bankado shirin wasu na kawo cikas a zaman lafiya a jihar.

Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri cewa wasu kungiyoyin addinai da siyasa na shirin rikita jihar kan shari'ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel