Dino Melaye da Tsohon Gwamna Sun Gwabza Kan Tinubu a Taron PDP, an Yaɗa Bidiyon

Dino Melaye da Tsohon Gwamna Sun Gwabza Kan Tinubu a Taron PDP, an Yaɗa Bidiyon

  • Yayin da ake ganawar shugabannin jam'iyyar PDP, tsohon gwamnan Binuwai da Sanata Dino Melaye sun gwabza
  • Melaye ya kalubalanci Samuel Ortom kan dalilin halartar taron duk da goyon bayan Shugaba Tinubu da ya yi
  • Hakan ya biyo bayan ganawar shugabannin jam'iyyar PDP na Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a jiya Laraba 27 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT Abuja - Sanata Dino Melaye ya caccaki tsohon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom kan goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Dino Melaye ya samu matsala da tsohon gwamnan na Binuwai ne yayin ganawar shugabannin jam'iyyar PDP a Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Dino Melaye ya caccaki tsohon gwamnan PDP da Wike da Atiku suka hadu, bidiyon ya yadu

Dino Melaye ya Fadi dalilin hatsaniyasa da tsohon gwamna kan goyon bayan Tinubu
Dino Melaye ya caccaki Samuel Ortom kan nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Dino Melaye, Terver Akase.
Asali: Facebook

PDP: Hatsaniya ta faru tsakanin Dino, Ortom

An yi ganawar ne a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu inda Melaye ya kalubalanci Ortom kan dalilin zuwansa wajen taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ke fayyace dalilin sabanin nasa da tsohon gwamnan na PDP.

"Meyasa Ortom zai halarci taron jam'iyyar PDP bayan zai goyi bayan Tinubu a zaben da za a yi a 2027."
"Wannan shi ne babban dalilin da ya jawo hatsaniya yayin taron shugabannin jam'iyyar PDP a Arewa ta Tsakiya."
"Ya ce ya yi mamaki yadda Ortom babu kunya ya shiga ganawar ya ke tafiyar kasaita duk da cin dunduniyar PDP da ya yi."

- Dino Melaye

Dino Melaye ya ce PDP ta dauki mataki

Melaye ya ce Ortom ba shi da kunya kuma ya kamata jami'yyar PDP ta ɗauki mummunan mataki kansa.

Kara karanta wannan

Binciken El-Rufai: An bayyana dalilin kafa kwamitin bin diddikin ayyukan tsohon gwamnan

Dukkansu sun yi wa juna ihu yayin da Ortom ya kaɗu da irin kalaman Melaye a gare shi, daga bisani ya yi magana ba tare da mayar masa da martani ba.

Kusoshin PDP sun goyi bayan Damagun

A wani labarin, kun ji cewa kutsoshin jam'iyyar PDP sun nuna goyon bayansu ga shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Umar Damagum.

Gwamnan Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu a birnin Tarayya Abuja..

Wannan na zuwa ne bayan tasa Damagum a gaba a kokarin neman tumɓuke shi daga kan kujerar shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel