Matakin da Gwamnatin Tinubu ta Dauka Ya Jefa Karatun Amaechi da Melaye a Hadari

Matakin da Gwamnatin Tinubu ta Dauka Ya Jefa Karatun Amaechi da Melaye a Hadari

  • A sakamakon hukunta jami’ar Baze da majalisar CLE ta yi, mutane da-dama sun shiga cikin gagari a Najeriya
  • Matsalar ta shafi fitattun ‘yan siyasa da ke zuwa jami’ar domin karo karatu musamman na digiri a shari’a
  • Tsohon ministan sufuri da Dino Melaye da ya yi takarar Gwamna a Kogi yana cikin masu shaidar LLB daga Baze

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar kula da ilmin shari’a (CLE) ta maka takunkumi a kan jami’ar Baze da ke birnin Abuja saboda saba dokar daukar dalibai.

Wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka ta karkasin majalisar CLE ya jefa dinbin mutane cikin tsaka mai wuya a cewar The Cable.

Baze.
Dino Melaye ya yi digiri a Jami'ar Baze Hoto: _dinomelaye
Asali: Twitter

CLE ta hana digirin shari'a a jami'ar Baze

Kara karanta wannan

An yanka ta tashi: Jerin jiga-jigan siyasa 4 da suka karanta shari'a a jami'ar Baze

Bayan daukan dalibai fiye da kima duk shekara, CLE ta zargi jami’ar da bada shaidar digirin ilmin shari’a a shekaru uku maimakon biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga yanzu zuwa shekaru biyar masu zuwa, jami’ar ba ta isa ta dauki daliban da za su karanta ilmin shari’a ba saboda sabawa ka’idojin.

Rahoton ya ce wannan hukunci da aka dauka a kan jami’ar Baze zai iya shafar wasu ‘yan siyasa da su ka yi digiri tsakanin wannan lokaci.

'Yan siyasan da su kayi digiri daga Baze

Hakan zai jawo alambar tambaya kan ingancin takardun shaidar karatun manyan ‘yan siyasa kamar Dino Melaye da ya yi takarar gwamna.

Rotimi Amaechi wanda ya yi Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari yana cikin daliban ilmin shari’a da jami’ar ta yaye a shekarar 2022.

Sanatan Anambra ta Kudu watau Ifeanyi Ubah ya samu shaidar digirin shari’arsa a 2021.

Kara karanta wannan

Kaciyar mata: Gwamnan PDP ya haramta al'adar a fadin jiharsa, an bayyana illarta ga mata

Haka zalila tsohon ministan harkokin jirgin sama, Osita Chidoka wanda jagora ne a PDP ya samu digirinsa na LLC ne daga jami’ar ta Baze.

Abin da ba a tabbatar ba shi ne ko hukuncin zai yi aiki a kan wadanda sun dade da kammala karatunsa a jami’ar kafin a dauki matakin.

Mafi yawan ‘yan siyasa suna zuwa jami’ar ne domin karo ilmi, sai dai dama tun can wasu suna ganin akwai abin dubawa a irin karatun na su.

"Malamai suka kawo APC" - Sule

A baya an samu labari cewa jigon PDP, Sule Lamido ya ce a tambayi wadanda su ka zabo APC da Muhammadu Buhari kan tsadar rayuwar yau.

Alhaji Sule ya ce malaman addini su ka kawo Muhammadu Buhari da Bola Tinubu kan mulki don haka su ne su ka jefa al’umma cikin wahala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel