Mace Ta Farko Ta Kafa Tarihin Zama Matamakiyar Kakakin Majalisar Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

Mace Ta Farko Ta Kafa Tarihin Zama Matamakiyar Kakakin Majalisar Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da mataimakin kakakin Majalisar jihar Kogi ya yi murabus, Majalisar ta zabi sabuwar matamakiyar kakakin
  • Hon. Ojoma Comfort Nwuchiola ita ta yi nasarar kasancewa sabuwar mataimakiyar kakakin Majalisar
  • Wannan na zuwa ne bayan mai rike da kujerar Hon. Enema Paul ya yi murabus saboda rashin lafiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Majalisar Dokokin jihar Kogi sun zabi mataimakiyar kakakin Majalisar don maye gurbin wanda ya yi murabus.

Majalisar ta zabi Hon. Ojoma Comfort Nwuchiola a matsayin mataimakiyar kakakin Majalisar bayan murabus din Hon. Enema Paul.

Mace ta zama mataimakiyar kakakin Majalisar jihar Arewa
Mace ta kafa tarihin zama mataimakiyar kakakin Majalisar jihar Kogi. Hoto: Yahaya Bello, Ojoma Comfort.
Asali: Facebook

Mene dalilin murabus din Hon Paul?

Hon. Paul ya yi murabus ne saboda rashin lafiyar da ya ke fama da ita wanda yake hana shi gudanar da ayyukan ofishin, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ni na taimaki APC ta ci mulki, gwamnan Arewa ya soki 'yan Majalisar Tarayya da Suka Sako Shi a Gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabuwar mataimakiyar kakakin Majalisar ta samu mukamin ne yayin zaman Majalisar a ranar Alhamis21 ga watan Disamba.

Ojoma ta fito daga yankin Kogi ta Gabas wacce ke wakiltar mazabar Ibaji a Majalisar jihar.

Yayin da tsohon mataimakin kakakinm Majalisar, Enema ya ke wakiltar mazabar Okura a Majalisar.

Enema ya ajiye mukamin ne yayin zaman Majalisar inda ya ba da hujjojin cewa ya na fama da rashin lafiya da ke hana shi ayyukansa.

Wane martani Ojoma ta yi?

Dan Majalisar ya na shan fama da jinyar wacce ba a bayyana ba tun shekarar 2011 inda ya sha fita kasashen ketare don neman lafiya, cewar Nigerian Pilot News.

Bayan ya yi murabus din, magatakardar Majalisar, Sule Ahmed Chogudo ya nemi masu neman kujerar don cike gurbi.

Daga bisani Ojoma ta yi nasara bayan bin dukkan ka'idojin zaben a Majalisar cikin tsanaki.

Kara karanta wannan

Kogi: Mataimakin shugaban majalisar dokoki ya yi murabus kan abu 1, an naɗa sabo nan take

Sabuwar mataimakiyar kakakkin Majalisar ta godewa Gwamna Yahaya Bello da kuma kakakin Majalisar kan wannan dama da ta samu.

Mataimakin kakakin Majalisa ya yi murabus

A wani labarin, Mataimakin kakakin Majalisar jihar Kogi, Hon. Enema Paul ya yi murabus daga kujerarshi.

Paul ya yi murabus ne saboda fama da rashin lafiya da ya dade ya na yi tun shekarar 2011.

Dan Majalisar ya bayyana cewa rashin lafiyar na damun rayuwarshi tare da hana shi gudanar da ayyukansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel