Peter Obi
Shugaban cocin INRI Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa za a zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar jam'iyyar hadakata a 2027.
A labarin nan, za ku ji cewa ana hasashen wasu daga cikin manyan da suka taru a ADC domin fatattakar gwamnatin Bola Tinubu za su nemi kujerar shugaban kasa.
Tsagin jam'iyyar LP ya bukaci Peter Obi ya fita daga tafiyarsu bayan halartar taron hadakar 'yan adawa a Abuja. LP ta ce ba za ta shiga hadakar 'yan adawa ba.
Mai magana da yawun kungiyar haɗaka, Bolaji Abdullahi ya ce sun zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita saboda tsarinta da manufofinta.
Peter Obi ya mika bukatar yin takara wa'adi daya ga gamayyar 'yan adawa a Najeriya. Obi ya ce zai yi takara sau daya ba tare da yin tazarce ba a 2031.
An hana su Atiku dakin taron kaddamar da ADC a Abuja ba zato ba tsammani. 'Yan adawar sun ce ba za su ja da baya ba yayin da suka zargi sa hannun gwamnati.
Ƙungiyar adawa ta Atiku ta zaɓi ADC don doke Tinubu a 2027, tare da naɗa David Mark da wasu ƙwararru a matsayin shugabanni, yayin da take kuma neman rajistar ADA.
Wasu 'yan jam'iyyar ADC a Najeriya sun yi watsi da maganar hadakar 'yan adawa da aka kulla. Sun ce ba a tuntube su ba kafin a yi maganar hadaka don kifar da Tinubu.
Jagoran jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya jaddada aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a zaben 2027. Ya ce zai yi wa'adi daya kawai idan ya samu nasara.
Peter Obi
Samu kari