Ba Zai Yiwu Obi Ya Yi Galaba Kan Atiku ba – Darektan Kamfe Ya Saki Hasashen Zabe

Ba Zai Yiwu Obi Ya Yi Galaba Kan Atiku ba – Darektan Kamfe Ya Saki Hasashen Zabe

  • Dele Momodu yana ganin babu ta yadda Peter Obi ko Bola Tinubu za su doke Atiku Abubakar a 2023
  • Darektan kwamitin yakin neman zaben na PDP ya ce Atiku zai samu karbuwa a jihohi 19 a Arewa
  • Momodu ya ce idan an shiga Kudancin Najeriya, ‘dan takaran na su yana bayan APC ko kuwa LP

Abuja - Darektan dabarun sadarwa a kwamitin yakin neman zaben PDP, Dele Momodu yana da ra’ayin cewa Atiku Abubakar yana hanyar nasara.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Arise a ranar Litinin, Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar zai samu akalla 25% a duka jihohin da ke Arewa.

Ganin dan takaran PDP a zaben 2023 ya fito daga yankin Arewacin Najeriya, ‘dan jaridar ya ce za su samu galaba kan sauran masu neman shugabanci.

Kara karanta wannan

Shugabannin Fulani Sun Tsaidawa 'Yan Kabilarsu ‘Dan Takara a Zaben Shugaban Kasa

A dokar kasa ana bukatar akalla 25% a jihohi 24 kafin a rantsar da ‘dan takara a matsayin shugaban kasa, Momodu ya ce Atiku zai cike sharadin nan.

Lissafin Darektan zaben Atiku a PDP

“Atiku zai samu 25% a duka jihohin Arewacin Najeriya. Kuma zai zarce jihohi 24 da ake nema daga ya samu karin biyar rak a Kudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yankin Kudu, a duk jihar da Obi zai zo na farko, Atiku ne zai zo na biyu. A duk inda Tinubu zai zo na farko, Atiku ne zai zo na biyu.

Sannan Atiku Abubakar zai yi galaba a wasu jihohin da ke Kudancin Najeriya.

Atiku
Atiku yana kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Obi da Tinubu ba za su kai labari ba?

A rahoton Vanguard an ji Momodu ya caccaki magoya bayan Peter Obi, ya ce ba su da mutanen da ke neman takara da za su taimakawa jam’iyyarsa ta LP.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku Ya Fada Mani Zai Yi wa Nnamdi Kanu a Kwana 100 na Farko a Ofis - Wabara

Momodu ya ce mafi yawan masu kaunar Tinubu su na tare da shi ne saboda shi Bayarabe ne, a cewarsa a Arewa babu wanda ake magana irin Atiku.

Jaridar The Cable da ta bibiyi hirar ta rahoto Darektan na kamfe yana cewa dole ayi la’akari da kabilanci domin yana tasiri wajen zaben da ake yi a kasar.

Ganin yankin Arewa ya fi yawan jihohi, jigon na PDP yana ganin idan mutumin Arewa da 'Dan Kudu suka tsaya takara, an san wanda zai yi nasara.

NNPP tana neman kuri'un Neja

Bayan ya ziyarci garuruwan Minna, Bida, da New Bussa, rahoto ya zo cewa ‘dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya je Kontagora da ke jihar Neja.

‘Dan takaran Shugaban kasa a Jam’iyyar adawar, ya je ya gaida sabon Sarkin Kontagora, Muhammad Barau kafin ya tallata NNPP ga magoya baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel