Atiku, Tinubu ko Obi: Tsohon Dan Majalisa, Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Ya Kamata A Samar Da Magajin Buhari

Atiku, Tinubu ko Obi: Tsohon Dan Majalisa, Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Ya Kamata A Samar Da Magajin Buhari

  • Sanata Shehu Sani ya ce yana ganin bai kamata a kakaba wa yan Najeriya shugaban kasa na gaba ba amma ba bari yan kasar su zabi wanda suke ta hanyar zabe na adalci, inganci da nagarta
  • Tsohon dan majalisar cikin wani rubutu da ya yi a Twitter ya yi kira ga yan siyasa su dena siyan kuri'u, yana mai cewa hakan zai iya shafar cigaban dimokradiyya a kasar
  • Wasu yan Najeriya sun yaba masa kan maganganu na hikima da ya yi a wannan mataki mai muhimmanci a kasar, wasu kuma suna ganin FG ta riga ta dakile yiwuwar siyan kuri'u saboda sauyin fasalin kudi na CBN

Tsohon dan majalisar Kaduna ta Tsakiya ya bayyana hanyar da ya kamata a bi don samar da shugaban kasa na gaba.

Ana yan makonni zaben shugaban kasa na 2023, Shehu Sani ya ce kamata ya yi dan siyasa ya samu mukami da hanyar kuri'a ba siya ba ko a sayar masa.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Kwankwaso Ya Fada Ma Yan Najeriya Abu 1 Da Za Su Yi Maimakon Tashe-Tashen Hankula

Shehu Sani
Atiku, Tinubu ko Obi: Tsohon Dan Majalisa Ya Bayyana Yadda Ya Kamata A Samar Da Magajin Buhari. Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shehu Sani ya yi magana kan zaben shugaban kasa na 2023, ya aika sako ga yan siyasan Najeriya

A cikin wata rubutu da ya wallafa a Twitter a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, Sani ya aika kalamai masu dauke da hukima ga yan siyasan Najeriya da jam'iyyun siyasa.

A rubutun na Twitter da Legit.ng ta gani ya ce:

"Ya kamata shugaban Najeriya na gaba ya fito ta hanyar zabe ba cinikayya ba. Bai kamata a siya ko sayar da mukamin siyasa ba.
"Raba kudade ga masu zabe don siyan kuri'a ba dimokuradiyya ba ne; lokaci ya yi da za a kawo karshen hakan."

Yan Najeriya sun yi martani

Yan Najeriya sun tafi shafin Twitter sun yi martani kan maganan na Shehu Sani.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

@Kayodeteslim ya rubuta:

"Toh ya ya batun yan takarar da suka samu tikiti ta hanyar siya?"

@TukunboAdesina ya ce:

"Dole a dakile siyar da kuri'a, ana bukatar nagarta a siyasa."

@ezecollinsa ya rubuta:

"Duk da cewa kana wata jam'iyyar daban amma ina ganin kana iya yi wa gwamnatin @PeterObi aiki domin cigaban Najeriya."

@Mr_DoubleImpact ya ce:

"Allah ya yi wa Najeriya tanadi."

@AtikuChangeDCh2 ya rubuta:

"Ka yi magana mai kyau, amma ya kamata mu bayyana karara cewa baya ga zabe, batun adalci, daidaito, gaskiya, hadin kai, zaman lafiya da girmama al'adu a Najeriya na da muhimmanci."

@Borninthevilla1 ya ce:

"Jam'iyyu guda uku sun tura wa wani N20,000 kowanensu, kamar ni ne kadai ban samu komai ba a wannan zaben."

A wani rahoton kuma, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnoni da ke rikici da shugabannin jam'iyyunsu da su koma jam'iyyar AAC su hada kai da Omoyele Sowore.

Asali: Legit.ng

Online view pixel