Kotu Ta Kori Karar da Ta Nemi a Hana Peter Obi Shiga Zaben 2023

Kotu Ta Kori Karar da Ta Nemi a Hana Peter Obi Shiga Zaben 2023

  • Kotun daukaka kara ta kawo karshen shari'ar da ake nemi ta tuge Peter Obi daga takarar shugaban kasa a inuwar LP
  • Jam'uyyar APM ce ta shigar da Obi da Labour Party ƙara tana mai kalubalantar sahihancin takararsa a zabe mai zuwa
  • Tsohon gwamnan jihar Anambra na ɗaya daga cikin manyan 'yan takara uku da ake hasashen zasu iya gaje Buhari

Abuja - Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta yi fatali da karar da jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta shigar tana rokon a kori Peter Obi daga takarar shugaban ƙasa a inuwar LP.

Da take yanke hukunci, Alkalin Kotun mai shari'a Monica Dongban-Mensan, ta fatattaki shari'ar bisa hujjar cewa APM ba ta da hurumin shigar da ƙarar Obi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana neman matar gwamna: Kotu ta mika dangin Yahaya Bello gidan yari kan badakalar N3bn

Peter Obi.
Kotu Ta Kori Karar da Ta Nemi a Hana Peter Obi Shiga Zaben 2023 Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Haka zalika Kotun ta ci tarar jam'iyyar APM kuɗi naira dubu N200,000 da za'a baiwa Labour Party da Peter Obi, waɗanda ake kara na biyu na uku a shari'ar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya shiga tseren kujerar shugaban ƙasa inda zai fafata da manyan takarar kamar Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da ya rage ƙasa da mako uku gabanin zaben shugaban kasa wanda zai gudana ranar 25 ga watan Fabarirun da muke ciki, masu neman kujera lamba a Najeriya na ci gaba da tallata kansu ga 'yan Najeriya.

Ana ganin cewa 'yan arewa ne raba gardama kan wanda zai gaje shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa don haka yan takarar suka fi maida hankali a shiyyoyi uku.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta yi hukuncin karshe kan sahihin dan takarar gwamnan APC a Kaduna

Kamar dai sauran 'yan takara, Mista Obi, ɗan asalin jihar Anambra a kudu maso gabas ya ɗauki abokin takararsa, Datti Baba Ahmed, ɗan asalin jihar Kaduna duk don samun kuri'an jama'a.

Dalilin Da Yasa Peter Obi Zai Samu Kuri'u da Yawa a Arewa a Zaben 2023

A wani labarin kuma jigon jam'iyyar LP ya yi hasashen tulin kuri'un da Obi zai samu daga arewacin Najeriya a zaɓen 2023

Ibrahim Abdulkareem, ya ce yan arewa na ciki fushi da halin da yan siyasa suka jefa su na rashin tsaro da fatara don haka zasu koma wajen Peter Obi.

A cewarsa, da yawan mutane na kallon ɗan takarar LP ba abakin komai ba amma zai ba da mamaki a ranar zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel