Abdulmumin Jibrin ya saduda, yana neman sulhu da shugabannin APC gabannin zaben da za a sake (bidiyo)

Abdulmumin Jibrin ya saduda, yana neman sulhu da shugabannin APC gabannin zaben da za a sake (bidiyo)

Rahotanni sun kawo ccewa dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa na kokarin ganin ya sasanta sabanin da ke tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano gabannin zaben da za a sake a mazabarsa a ranar Asabar.

An gano dan majalisar wanda ya raba jihad a jami’an jam’iyyar ciki hara gwamnan jihar a cikin wani bidiyo yana yiwa Shugaban jam’iyyar, Alhaaji Abdullahi Abbass fadanci a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Bidiyon wanda ya yi fice a shafukan sadarwa, ya zo wa magoya bayan APC da dama, musamman wadanda ke cikin rikicin da ke tsakanin dan majalisar da shugabancin jam’iyyar.

Idan dai za ku tuna an zargi Kofa da cin dunduniyar jam’iyyar a 2019 wanda hakan ya sanya aka dakatar dashi. Hakan ya kawo rigima a tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tun bayan da ya yi nasara a zabensa, sai Kofa ya watsar dda APC har said a kotun daukaka kara a jihar Kaduna ta soke zabensa sannan ta yi umurnin sake sabon zabe a mazabarsa.

KU KARANTA KUMA: Sanata Nazif ya ce babu makawa sai PDP ta kwato kujarar Shugaban kasa a 2023

Amma tun bayan soke zabensa, sai Kofa ya fara shiga cikin manyan jam’iyyar kamar su Governor Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da kuma Shugaban jam’iyyar, Alhaji Abdullahi Abbas a kokarinsa na samun goyon bayansu.

Sannan bayan kotun koli ta yanke hukuncinta kan zaben gwamna na 2019, an gano Kofa a gidan gwamnatin Kano don taya Ganduje murna.

Ya kuma kasance a filin jirgin sama tare da wasu manyan yan siyasa a jihar don tarbar Shugaban APC a lokacin da ya dawo daga Abuja, kwanaki biyu bayan hukuncin kotun koli da ta tabbatar da zaben Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel