TY Danjuma ya sayi Otal din kasar Ingila da aka gina shekaru 300 da suka wuce
Tsohon ministan tsaron Najeriya, Theophilus Danjuma, ya sayi wani Otal mai shekaru 300 a garin London na kasar Ingila a kan kudi Naira biliyan daya.
Jaridar Bloomberg ta bayyana cewa tsohon ministan, wanda aka fi kira da TY Danjuma, na daga cikin masu kudin duniya da suka mallaki biliyoyin daloli. Jaridar ta ce TY Danjuma ya mallaki Dalar kasar Amurka biliyan daya da miliyan dari biyu ($1.2bn).
Tsohon Otal din da TY Danjuma, mai shekaru 80 a duniya, ya saya na dauke da dakuna goma sha hudu (14) ne kacal.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Kotun sauraron korafin zabe ta yi watsi da wata bukatar Buhari da INEC
Toshon Otal din mai suna 'Kings Arms' da aka gina shekaru 300 da suka gabata ya na daf da kotun Hampton a birnin London kuma ya taba zama gida ga sarkin Ingila, Henry VIII, a shekarar 1509.
Yanzu haka ana yi wa Otal din kwaskwarima. Ana saka ran bayan kammala gyare-gyaren, za a ke biyan kudin kasar Ingila Yuro 250 duk kwana daya a dakin Otal din.
A shekarar 1998, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, marigayi janar Sani Abacha, ya bawa TY Danjuma kyautar rijiyar man fetur.
Ya bar aikin soja a shekarar 1979 tare da shiga harkar kasuwancin man fetur da safarar kaya ta hanyoyin ruwa. Ya hada gwuiwa da kamfanonin dillancin man fetur na Total SA da Petrelo Brasileiro.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng