"Kwankwaso ne Mai Falle 1": Shugaban Hukuma Ya Yi Watsi da Tasirin ADC a Kano
- Ana ci gaba da samun martani tun bayan da jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam'iyyar ADC
- A zantawarsa da Legit a Kano, Shugaban hukumar KASA, Kabiru Dakata ya ce sauya shekar Kwankwaso ya fitar da gwamna daga zargi
- Ya bayyana cewa, an so a goga wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kashin kaji a lokacin da ya ce akwai babbar matsala a cikin NNPP
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Shugaban hukumar tallace-tallace da dangoginsu, Kabiru Dakata ya bayyana cewa sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta fito da matsalolin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hango a NNPP.
A zantawarsa da Legit a ranar Talata, 31 ga watan Maris, 2026, Dakata ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha nanata cewa akwai babbar matsalar shugabanci a NNPP.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa a ranar Litinin, 30 ga watan Maris na shekarar 2026 ne Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu 'yan Kwankwasiyya suka sauya sheka zuwa ADC.
Sauya shekar Kwankwaso ta wanke Abba - Dakata
A tattaunawarsa da Legit Hausa, Dakata ya bayyana cewa sauya shekar Kwankwaso zai jawo tambayoyi da dama daga Kanawa da ke bin lamarin siyasar jihar.
A kalamansa:
"Yau idan Kwankwaso ya yi ta gaya mana maganganu cewa fitarmu daga NNPP cin mutunci ne, butulci ne, cin amana ne domin ya shafa mana kashin kaji a wajen al'ummar jihar Kano."
"Sai yau aka wayi gari shi kan shi ya fita daga jam'iyyar NNPP, saboda haka al'ummar jihar Kano ne za su tambaye shi, kai me ya sa ka fita? Idan ya ce akwai rigingimu a cikin jam'iyyar, sai su ce to me yasa ka kalubalanci Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf don ya fita da jama'arsa?"
Ya bayyana cewa sun fi kowa farin ciki da Sanata Kwankwaso ya bar NNPP zuwa ADC saboda hakan ya gaskata Gwamna Abba Kabir Yusuf na cewa akwai matsala.
Dakata ya kara da cewa babu wani tasiri da ADC za ta yi da zai girgiza damar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba, domin mutanen Kano suna ganin abubuwan da ya ke masu.
Dakata: Abba zai koma kujerarsa a Kano
Kabiru Dakata ya bayyana cewa tun bayan da gwamna ya sauya sheka zuwa APC al'ummar Kano ke samun sauyi mai kyau.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa:
"Aikin wuju-wujun da ya gagari gwamnoni, ya gagari gwamnatin Kwankwaso ya gagari wasu gwamnatoci a baya, ga shi yanzu gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf zai yi aikin wuju-wuju a sama wa mutane sa'ida."
Dakata ya bayyana cewa yanzu haka an daina siyasar daba da tashin hankali a Kano, wanda aka ga misali a zaben da ya gabata, wanda ko kuda ba a kashe ba.
Shugaban hukumar KASA ya nanata cewa mutanen Kano suna ganin aikin da Abba ya ke masu, kuma tabbas za su mayar da shi kujerar gwamna.
Ya kara da cewa Sanata Kwankaso ne mai falle daya, musamman ganin bai iya zarcewa a mulkin Kano ba kamar yadda Malam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje.
NNPP za ta yi aiki da ADC
A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar adawa ta NNPP ta bayyana shirin haɗin gwiwa da ADC domin a yi wa APC rubudgu a babban zaɓe mai zuwa da za a yi 2027.
Duk da jagoran jam'iyyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bar NNPP, ana nuna ana tare da shi kuma za a ci gaba da aiki tare a babban zabe mai zuwa.
Jim kadan bayan Kwankwaso ya yanki tikitin zama halastaccen ɗan ADC, NNPP ta bayyana irin tattaunawar da aka yi da su kafin Sanatan ya canja jam'iyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


