Kwankwaso, Atiku, Obi Sun Hade Kai, Sun Shirya Kayar da Tinubu a Zaben 2027
- Manya-manyan 'yan takarar shugaban kasa na 2023 sun hadu a jam'iyyar ADC domin fuskantar zaben 2027, inda za su fafata da APC
- Masu sharhin siyasa na ganin cewa rashin hadin kan wadannan jagorori a zaben baya ne ya ba Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaben
- Yanzu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma ADC, ana ganin cewa hada takararsa da Peter Obi ita za ta ba jam'iyyar nasara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A wani mataki da ake ganin zai sake rura wutar siyasar adawa a Najeriya gabanin zaɓen 2027, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga NNPP.
Wannan mataki ya share fage ga Kwankwaso wajen haɗewa da sauran manyan jigajigan adawa a jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC domin kalubalantar jam'iyyar APC mai mulki.

Source: Facebook
ADC: Kwankwaso ya hadu da Atiku, Obi
A halin yanzu, jam'iyyar ta ADC ta zama matattarar manyan 'yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi, David Mark, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai, Rauf Aregbesola da sauransu, in ji rahoton Daily Trust.
Masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa rashin irin wannan kawance a zaɓen 2023 ne ya sa jam'iyyun adawa suka gaza samun nasara akan Shugaba Bola Tinubu.
Idan aka haɗa ƙuri'un da Atiku (6,984,520), Peter Obi (6,101,533), da Kwankwaso (1,496,687) suka samu a 2023, sun zarce na Tinubu (8,794,726) nesa ba kusa ba.
A cewar masana, wannan sabon haɗin kai ya dawo da fatan masu adawa waɗanda suka fara karaya kan yiwuwar kayar da jam'iyyar APC dake ƙara samun ƙarfi a faɗin ƙasar nan.
Tasirin sauya shekar Kwankwaso a Kano
Jihar Kano tana ɗaya daga cikin jihohin da ƙuri'unsu ke sauya fasalin zaɓe, kuma sauya shekar Kwankwaso daga NNPP ta nuna cewa har yanzu jam'iyyar APC ba ta mamaye jihar gaba ɗaya ba.
Duk da sauya sheƙar Gwamna Abba Yusuf zuwa APC, masana na ganin cewa Kwankwaso ne ke riƙe da madafun ikon zaɓe a jihar Kano ta hanyar ƙungiyar Kwankwasiyya.
Majiyoyi sun bayyana cewa:
"An yi yunƙurin lallashin Kwankwaso ya koma APC, amma yarjejeniyar ba ta kullu ba, wanda hakan ya sa ya zaɓi haɗa kai da sauran masu adawa a ADC."
Manufar "Save Nigeria Project"
Mataimakin kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Mansur Kurugu, ya bayyana cewa matakin na Kwankwaso ba na son rai ba ne, face domin kishin ƙasa da samar da canji.
Ya ce matakin yana ƙarƙashin inuwar "Save Nigeria Project", wani gagarumin shiri dake da nufin magance matsalolin da suka addabi Najeriya a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Mansur Kurugu ya jaddada cewa Kwankwaso a shirye yake ya marawa duk wanda ya fito a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na wannan gagarumin kawance baya.
A cewarsa:
"Ba mu shiga ADC don lallai sai an ba Kwankwaso takara lallai ba, mun dauki wannan mataki ne domin mu tabbatar da cewa an samar da adawa guda ɗaya mai ƙarfi."

Source: Twitter
Yiwuwar tikitin Obi/Kwankwaso a ADC
Mabiyan Peter Obi sun fara bayyana ra'ayin cewa hadakar Obi da Kwankwaso ita ce mafita mafi dacewa ga jam'iyyar ADC a zaben, in ji rahoton BBC.
Ziyarar da Peter Obi ya kai wa Kwankwaso a birnin Kano lokacin bikin Sallah ta nuna alamun hadin kai tsakanin manyan 'yan siyasar.
Yunusa Tanko, wanda shi ne kakakin ƙungiyar 'Obidient Movement' a Najeriya, ya amince da cewa batun tikitin haɗin gwiwa tsakanin Obi da Kwankwaso yana ƙara samun goyon baya a faɗin ƙasar.
Kwankwaso ya shiga ADC a hukumance
Tun da fari, mun ruwaito cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rajistar zama 'dan jam'iyyar ADC a hukumance tare da karbar katin mamba a Kano.
Manyan 'yan siyasa kamar Peter Obi da David Mark da Aminu Tambuwal sun halarci taron karbar Kwankwaso zuwa jam'iyyar 'yan adawa.
Tsohon gwamnan jihar na Kano ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar NNPP ne domin samar da sabon tsarin siyasa da zai tafi da kowa a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


