An Yi Musayar Kalamai yayin da Gwamna Sule Ya So Jawo Fintiri da Saraki zuwa APC

An Yi Musayar Kalamai yayin da Gwamna Sule Ya So Jawo Fintiri da Saraki zuwa APC

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya halarci wani taron kaddamar da littafi kan Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
  • A yayin taron, Gwamna Sule ya yi yunkurin zawarcin Gwamna Fintiri ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
  • Sai dai, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya gaggauta yin martani ga Gwamna Sule kan zawarcin gwamnan na PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya fito fili ya yi kokarin lallashin takwaransa na jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da ya shiga jam’iyyar APC.

Amma dai tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya gaggauta yin watsi da wannan tayin, inda ya jaddada cewa Ahmadu Fintiri ba zai bar jam'iyyar PDP ba.

Gwamna Sule ya yi zawarcin Saraki da Fintiri zuwa APC
Bukola Saraki, Gwamna Ahmadu Fintiri da Gwamna Abdullahi Sule Hoto: Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce wadannan musayar kalaman siyasa sun gudana ne a Yola yayin bikin kaddamar da littafi mai taken “Fintiri: The Man They Couldn’t Stop”, wanda Solomon Kumarga ya rubuta, a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

APC ta sake taso da batun sauya shekar Kwankwaso zuwa cikinta, ta fadi tanadin da ta yi masa

Gwamna Sule ya yi zawarcin Fintiri

Da yake jawabi a matsayin shugaban taron, Gwamna Sule ya yabawa salon shugabancin Fintiri da yadda yake tafiyar da mulki, inda ya bayyana shi a matsayin gwamna mai “APC DNA”, yana mai alakanta nasarorinsa da akidar ci gaba ta jam’iyyar APC.

"Dan’uwana, kana aiki kamar cikakken gwamnan ci gaba, kuma zan iya cewa APC na cikin jininka. Muna tafiya ne a hanya daya da kai."
"Ina ganin Mai Girma Gwamna ya ga yadda muke zuwa Delta, Rivers, Enugu, Plateau da Taraba, kuma kwanaki biyu da suka wuce mun je Kano. Wa ya sani, watakila wannan ziyara ta zama wata dama da zan kama wani babban kifi.”

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Sule ya yi guzirin hulunan APC

Gwamna Sule ya ce ya zo da hular APC, yana mai nuni da cewa zai iya sanya ta a kan Fintiri idan gwamnan “yana tunanin sauya sheka,” inda ya kara da cewa da ya san Saraki zai halarta, da ya kawo huluna biyu.

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi, Shettima ya karbi gwamnan da ya shiga jam'iyyar a hukumance

Da yake magana cikin yanayin raha da fahimtar juna, Gwamna Sule ya ce ya san nauyin shugabanci, ya kuma yabawa Fintiri kan juriya da jajircewarsa a ofis.

Saraki ya yi wa Gwamna Sule martani

Da yake mayar da martani, Bukola Saraki, wanda shi ma ya halarci taron, ya yi watsi da yunkurin daukar gwamnan, yana mai cewa tawagar APC za ta koma gida da hulunan da ta zo da su, shafin @NigAffairs ya sanya bidiyon maganar.

"Ba na son na mayar da martani ga shugaban taron, amma kuma ba zan yi shiru ba. Shugaban taron ya ce ya zo da wasu huluna. Ina tabbatar muku cewa za ku koma gida da wadannan hulunan.”

- Bukola Saraki

Gwamna Sule ya yi zawarcin Fintiri zuwa APC
Gwamna Abdullahi Sule tare da Gwamna Ahmadu Fintiri a wajen kaddamar da littafi Hoto: Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Meyasa APC ke son jawo gwamnonin PDP?

Saraki ya kara da cewa sha’awar APC ga gwamnonin PDP shaida ce ta kyakkyawan aikinsu.

"Idan ba ma aiki yadda ya kamata, ba za ku yi kokarin daukar mu ba. Ganin kuna kokarin daukar su, hakan na nufin suna aiki tukuru.”

- Bukola Saraki

Saraki ya yi kokarin ganin ya sasanta rikicin da ya barke a PDP musamman daga zaben 2023, sai dai kusan kwamitin na shi bai samu nasarar hana gwamnoni sauya-sheka ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano: Binciken Ganduje na nan duk da Abba ya shigo jam'iyyar APC

Batun sauya Shettima a tikitin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan batun sauya Kashim Shettima a zaben 2027.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta fara tattaunawa kan tikitin mataimakin shugaban ƙasa na zaɓen 2027 ba.

A cewarsa, yawancin labaran da ke yawo a kafafen watsa labarai kan batun sauya mataimakin shugaban ƙasa a zabe mai zuwa ba su da tushe balle makama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng