Kwankwaso da Wasu Manyan Yan Siyasa 3 da Suka 'Ci Amanar' Iyayen Gidansu a Kano

Kwankwaso da Wasu Manyan Yan Siyasa 3 da Suka 'Ci Amanar' Iyayen Gidansu a Kano

Kano, Nigeria - Danbarwar siyasar jihar Kano na ci gaba da jan hankali tun bayan bullar labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga Kwankwasiyya da NNPP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wannan al'amari ya ja hankalin gaba daya fagen siyasar Najeriya, musamman ganin cewa gwamnan na shirin rabuwa da ubangidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Abba da Kwankwaso.
Gwamna Abba Kabur Yusuf tare da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2025, Gwamna Abba ya kawo karshen duk wata jita-jita, ya koma jam'iyyar APC mai mulki a hukumance, kamar yadda The Cable ta kawo.

Sai dai duk da haka, gwamnan bai ce komai game da alakarsa da Kwankwaso ba, amma dai alamu sun nuna kowa zai iya kama hanyarsa a zaben 2027.

A nasa bangaren, jagoran NNPP na kasa, Kwankwaso ya bayyana cewa wannan abu da Abba Gida-Gida ya yi cin amana ne, inda ya yi ikirarin cewa zai yi nadama a gaba.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin Kwankwaso ya ci amanar ubangidansa a jihar Kano

Legit Hausa ta tattaro cewa a tarihin siyasar Kano, wannan ba shi ne karo na farko da ake babewa tsakanin ubangida da yaronsa ba, shi kansa Kwankwaso ana zargin ya ci amanar ubangidansa.

Bisa haka, mun tattaro muku duka bayanan da ya kamata ku sani sani game da wadanda ake zargi da wadanda aka tabbatar da sun rabu da iyayen gidansu a siyasar Kano.

1. Kwankwaso da iyayen gidansa

Rabiu Musa Kwankwaso yana cikin wadanda ake ganin sun ci amanar wadanda suka daga shi a siyasa tun daga 1992 da ya samu damar zuwa majalisar wakilan tarayya.

Alfarmar wadannan manya ne ya shiga sahun wadanda suka yi zama domin fito da kundin tsarin mulki har kuma ya zama zababben gwamnan Kano a Mayun 1999.

  • Kwankwaso da Sanata Hamisu Musa

Tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin manyan 'yan siyasar da ake zargin sun ci amanar iyayen gidansu.

Ana dai zargin Kwankwaso da cin amanar Sanata Hamisu Musa, wanda ake ganin ya taimake shi a siyasance, kuma wannan zargi ya kara tasowa a dambarwar siyasa da ke faruwa a Kano kwanan nan.

Kara karanta wannan

Ana batun sauya shekar Abba, za a bayyana asalin wadanda suka ci amanar Kano

Sai dai a wani faifan bidiyo da tashar Siyasarmu TV ta wallafa, Injiniya Kwankwaso ya musanta wannan zargi, yana mai cewa sabanin fahimta ne ya shiga tsakaninsu.

"Har yanzu bana jin dadin wannan abu, tare muke komai da Sanata, safe dare duk muna tare, wata rana mun rabu da shi da nufin zamu yi wata tafiya washe gari.
"Da aka zo lokacin, ya zo gidana a Abuja, ina zaune a falo tare da mutane, sai na yi tunanin bari na gama da su kafin shi kuma mu fita da shi a mota, sai aka samu wata matsala, a lokacin ya zo da iyalinsa.
"Ni na yi tunanin bari na gama ganin mutane, ita iyalinsa sai aka tafi da ita sama wurin iyalina, sai aka tarar suna Sallah, hakan ya sa suka dauka kamar wani shiri aka yi. Bayan na gama na fito nace ina sanata, aka ce ya tafi.
"Na kira shi a waya ya ki dauka, na sa aka kira shi ya ce sun yi nisa ba za su dawo ba, na rasa yadda zan yi. Tun wannan abu, mutane da yawa sun sa baki har su Sarkin Dawaki don a ba shi hakuri, amma ya ki hakura."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan cewa ya hada baki da Abba wajen shiga APC

- Rabiu Kwankwaso.

Jagoran NNPP.
Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana cewa ba da niyya ya yi wa Hamisu Musa haka ba, kuma ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ya ba shi hakuri amma ya gagara hakura.

Ya ce tun da suke tare, bai taba cin amanarsa ba har zuwa ranar da wannan abu ya faru, wanda shi ne sanadiyyar samun sabaninsu.

  • Kwankwaso da Muhammad Dangalan

Bayan Sanata Hamisu Musa, ana kuma zargin Kwankwaso da cin amanar Muhammadu Dauda Dangalan, wanda ake ganin ya taimaka masa matuka wajen kafuwa a siyasa.

A wani bidiyo da shafin Amon Gaskiya ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya karyata wannan zargi, yana mai cewa sun yi zaman lafiya da Dangalan kuma sun rabu lafiya.

"Tun da muka fara siyasa a 1991, su (Dangalan) ne shugabanninmu amma maganar gaskiya ita ce, babanmu Dangalan mun zauna lafiya mun rabu lafiya."
  • Kwankwaso da Musa Gwadabe

Har ila yau, Kwankwaso ya musanta zargin da ake na cewa ya ci amanar Malam Musa Gwadabe, daya daga cikin manyan 'yan siyasar da ake ganin sun taimake shi.

Kara karanta wannan

Zance ya fito, an ji matakin da za a dauka kan mataimakin gwamnan Kano idan ya ki komawa APC

A lokacin da ya karbi bakuncin 'yan Kwankwasiyya daga karamar hukumar Fagge a jihar Kano, Kwankwaso ya ce tun da yake da Malam Musa, bai taba fada masa bakar magana ba.

"Tun da nake da Malam Musa Gwadabe, bai taba fada mini bakar magana, ni ma ban taba fada masa bakar magana ba, ko da za su barmu su koma jam'iyyar ACN, sai da ya kira ni ya fada mani," in ji Kwankwaso.

Kwankwaso ya ce har Musa Gwadabe ya koma ACN amma ba su daina mu'amala ta mutunci ba har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa.

Kwankwaso.
Jagoran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook
  • Kwankwaso da Abubakar Rimi

A wani bidiyo da Arewa Updates ta wallafa, Kwankwaso ya bayyana cewa babu inda ya ci amanar Abubakar Rimi kamar yadda ake yadawa.

Madugun Kwankwasiyya ya bayyana cewa mutanen Rimi ba su yi shi ba ko a lokacin zaben fitar da gwani na zaben 1999, amma duk da haka an hada kai kuma ana mutunta juna.

Tsohon gwamnan ya karkare da cewa duk masu yada labaran cewa ya ci amanar wadannan mutanen, sun rasa abin da za su fada ne wanda zai jawo ma Kwankwaso bakin jini.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi mafitar da Kwankwaso ke da ita bayan tafiyar Abba

Kwankwaso yana da tsohuwar alaka da Rimi, kuma yana dalibi a Kaduna sabanin santsi da tabo ya auku.

2. Abubakar Rimi da Malam Aminu Kano

Tarihi ya nuna cewa Abubakar Rimi ya zama gwamnan Kano a jamhuriya ta biyu ne bisa goyon bayan Malam Aminu Kano, wanda ya dauko shi a lokacin da shi ba kowa ba ne a fagen siyasa.

Sai dai bayan ya dare kan karahar mulki, yan siyasar da ke kewaye da Abubakar Rimi suka zuga shi, ya balle daga gidan siyasar Malam Aminu Kano.

A wata hira da Daily Trust ta yi da Sanata Rufa'i Hanga, mai wakiltar Kano ta Tsakiya, yacve abin da ya faru tsakanin Rimi da Malam Aminu darasi ne ga yan siyasa masu cin amana.

Sanata Hanga ya ce:

"Ina iya tunawa a zamanin Rimi, shi ba kowa ba ne a harkokin siyasa. Ya dawo ne daga aikin diflomasiyya a kasashen waje; shi ba dan siyasa ba ne, kuma a wata fuskar, kaddara ce ta sa aka dauko shi.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki zafi, Gwamna Abba ya kori hadiminsa bayan ya koma tsagin Kwankwaso

"Malam Aminu Kano ya nada shi domin ya zama gwamna. Sai dai wasu 'yan siyasa da suka kewaye Rimi suka zuga shi ya yi wa Malam Aminu Kano tawaye a siyasance."
"Rimi ya kasance sananne ne sosai, mai iko, ana kaunarsa sannan akasarin mutanen Kano suna girmama shi. Amma lokacin da ya ci amanar ubangidansa, mutanen Kano suka yi watsida shi."

Rimi ya bijire wa Malam Aminu Kano kuma a karshe ya yi murabus daga kujerar gwamna da ya bar jam'iyyar PRP wanda ta rabu zuwa bangaren santsi da tabo a 1981.

A karshe Rimi wanda aka zarga da bin gwamnatin Shehu Shagari ya sha kashi a zaben 1982 a hannun Sabo Bakin Zuwa duk da Malam ya rasu kafin a shiga filin takara.

3. Ibrahim Shekarau da Muhammadu Buhari

Ana ganin tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau na cikin manyan 'yan siyasar Kano da suka balle daga jikin iyayen gidansu duk da irin taimakon da suka masu har suka ci zabe.

Malam Shekarau ya raba gari da tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, wanda ake ganin farin jininsa, da kaunar da 'yan Arewa ke masa ta sa ANPP ta ci zaben gwamnan Kano a 2003.

Kara karanta wannan

'Abin da na fada wa Abba Kabir game da butulce wa Kwankwaso - Sanatan NNPP'

Sai dai bayan wannan zabe, aka samu matsala tsakanin Shekarau da Buhari, wanda ya kai ga ballewar gwamnan Kano na wancan lokacin daga ubangidansa, Buhari.

A wata hira da The Nation ta yi da tsohon hadimin Dr. Abdullahi Ganduje, Salisu Tanko Yakassai, ya ce rikicin da aka samu tsakanin Shekarau da Buhari ne ya kai ga kafa jam'iyyar CPC.

Shekarau da Buhari.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Malam Ibrahim Shekarau Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Ya ce:

"Shugaba Buhari bai ci zaben 2003 ba, amma jam’iyyarmu, ANPP ta lashe zaben gwamna a jihar Kano, wanda ya kai ga kafa gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau.
"Amma jim kadan bayan hakan, an samu sabani tsakaninsa da Shugaba Buhari, wanda daga baya bayan zaben 2007 ya kai ga samar da sabuwar jam’iyyar siyasa da Buhari ya kafa, wato CPC."

Farin jinin Buhari ya ba Shekarau damar doke PDP a zaben gwamnan Kano a 2003, amma sai ga shi a 2011, gwamnan na Kano yana yakar marigayin a takarar shugaban kasa.

4. Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje

Rabuwar Abdullahi Ganduje da Rabiu Kwankwaso na cikin rikicin siyasar yaro da ubangidansa mafi daukar hankali a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso

A rahoton da BBC Hausa ta tattaro, ta bayyana Ganduje a matsayin babban yaron Kwankwaso, wanda suka sha gwagwarmayar siyasa tare kuma suka mulki Kano tare.

Kwankwaso ya dauki Ganduje a matsayin mataimakinsa a zaben gwamnan Kano na 1999, haka kuma bayan ya dawo a 2011, madugu ya sake daukar Ganduje ya masa mataimkin gwamna a Kano.

Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso.
Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje Hoto: Saifullahi Hassan, Dr. Abdullahi Ganduje
Source: Facebook

Bayan karewar wa'adinsa a 2015, Kwankwaso ya tsayar da Ganduje takarar gwamna kuma ya mara masa baya har ya samu nasara a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Ganduje ya rabu da Kwankwaso bayan kafa gwamnati a shekarar 2015, hakan ya sa manyan jiga-jigan biyu suka zama manyan abokan hamayya a jihar Kano.

Madugun na Kwankwasiyya ya kwashi mutanensa daga APC zuwa PDP a 2018. Bayan gwabzawarsu a zaben 2019, sun yaki mutanen Ganduje a 2023 a karkashin NNPP.

5. Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da surukinsa kuma jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso sun shafe fiye da shekaru 40 tare a siyasa.

Sai dai a makon jiya, Gwamna Abba ya mika takardar ficewa daga jam'iyyar NNPP, wacce ta kawo shi kan mulki a zaben 2023 da taimakon Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya, in ji rahoton This Day.

Kara karanta wannan

"Ba za a ci amana da ni ba:" Kwankwaso ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba

Wannan lamari ya girgiza siyasar jihar Kano da ma Najeriya baki daya duba da yadda Kwankwaso ya sha wahala tun daga zaben 2019 har zuwa lokacin da Abba ya yi nasara a 2023.

Abba da Kwankwaso.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabur Yusuf tare da ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi ikirarin cewa komawar Abba APC ta ba shi mamaki matuka, domin a wani lokacin ya kan yi tunanin kamar mafarki ne, inda ya bayyana lamarin da tsantsar butulci da cin amana.

Har yanzu dai Gwamna Abba bai ce komai game da Kwankwaso duk da ya koma APC, amma ya jaddada cewa ya dauki wannan matakin ne saboda kishin jihar Kano.

Kwamishinoni 5 da suka bar tsagin Abba

A wani rahoton, kun ji cewa bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, wasu kwamishinoni akalla biyar sun yi murabus daga mukamansu.

Kwamishinonin sun dauki wannan mataki ne domin jaddada mubaya'arsu ga jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso kuma ba za su bi tawagar Abba zuwa APC.

Daga cikin wadanda suka ajiye aiki har da dan Madugun Kwankwasiyya, Mustapha Rabiu Kwankwaso da wasu kwamishinoni guda hudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262