Kano: Shekarau Ya Ƙi Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja Bayan Gano Maƙarƙashiyar Da Aka Shirya Masa

Kano: Shekarau Ya Ƙi Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja Bayan Gano Maƙarƙashiyar Da Aka Shirya Masa

  • Sanata Ibrahim Shekaru mai wakiltan Kano Central ya ki amsa gayyatar Gwamna Abdullahi Ganduje na zuwa Abuja ganin Shugaba Buhari a Abuja
  • Rahotanni sun nuna cewa Ganduje ya bi Shekarau har gidansa a daren ranar Juma'a da nufin su tafi Abuja ganin Buhari game da fitarsa daga APC
  • Wasu na kusa da Shekarau sun ce da farko ya yi niyyar tafiya Abujan amma sai ya gano ba Shugaban APC Abdullahi Adamu da wasu gwamnoni ne ke son ganawa da shi ba Shugaba Buhari ba

Kano - Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano Central, Ibrahim Shekarau, ya ki amsa gayyatar zuwa ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari na a yunkurin dakatar da fitarsa daga APC zuwa NNPP.

Daily Trust ta rahoto cewa an mika wa Shekarau gayyatar ne ta hannun Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Shekarau Ya Fasa Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja, Ya Gano Maƙarƙashiya Da Aka Shirya Masa
Shekarau ya ƙi amsa gayyatar 'bogi' da Ganduje ya masa na zuwa Abuja ganin Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Da farko, an yi wa Ganduje ihu a lokacin da ya ziyarci gidan Shekarau da ke Mundubawa domin shawo kansa ya bi shi su shiga jirgin sama su tafi ganin shugaban kasa a Abuja misalin karfe 1 na daren Asabar.

Abin da yasa Shekarau ya fasa zuwa Abujan

Duk da cewa da farko Shekarau ya amince zai tafi Abujan, wasu na kusa da shi sun shaida wa Daily Nigerian cewa Shekarau ya fasa tafiyar ne bayan ya gano da shugaban kasar bane ke son ganinsa amma shugaban APC, Abdullahi Adamu da wasu gwamnoni ne.

Ba a samu Mallam Shekarau ba a wayansa tun bayan da ya kammala shirin koma wa jam'iyyar NNPP. Don haka suna kokarin tafiya da shi Abuja domin su shawo kansa ya fasa komawa NNPP.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

"Sun san cewa Mallam yana girmama shugabanni, kuma ba zai ki amsa kirar shugaban kasa ba. Wannan shine dalilin da yasa suke yi wannan dabarar.
"Amma maganan gaskiya shine Mallam ya kai matakin da ba zai canja shawararsa ba. Idan ya koma APC, ina tabbatar maka kashi 80 cikin 100 na magoya bayansa za su koma NNPP.
"Kuma ko sun bashi tikitin takara ba tare da hamayya ba, ba zai iya cin zabe ba a APC," a cewar majiyar.

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel