Zaben 2027: Ana Neman Tinubu Ya Dawo da Nasir El Rufa'i cikin Jam'iyyar APC
- Wani tsohon ɗan takarar gwamna a Kebbi ya nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta shawo kan Nasir El-Rufai ya koma APC
- Ya ce sauye-sauyen siyasa a Arewa maso Yamma sun bar shugaban ƙasa ba tare da manyan abokai masu ƙarfi ba a yankin
- Malam Salihu Isa Nataro ya yi nuni da cewa dawowar Nasir El-Rufai na iya ƙarfafa tasirin APC da tara ƙuri’u a zaben 2027 da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Kebbi, Malam Salihu Isa Nataro, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin dawo da Nasir el-Rufai cikin jam’iyyar APC.
Nataro, wanda ya taɓa tsayawa takarar gwamna a Kebbi a ƙarƙashin APC, ya bayyana cewa yanayin siyasar Arewa maso Yamma na bukatar matakan gaggawa domin ƙarfafar shugaban ƙasa a yankin.

Source: Facebook
The Guardian ta rahoto ya ce bayan sauke Dr Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC, yankin Arewa maso Yamma ya rasa wani babban ginshiƙi da ke iya jan ragamar goyon bayan Tinubu.
Dalilan kiran dawo da Nasir El-Rufai APC
Nataro ya bayyana cewa sake daidaita ƙungiyoyin siyasa a Arewa na nuna cewa dole ne Shugaba Tinubu ya ɗauki Arewa maso Yamma da muhimmanci fiye da da.
Ya ce babu wani jigo mai ƙarfi a yankin da ke da cikakken tasiri wajen tara ƙuri’u ga shugaban ƙasa, lamarin da ke buƙatar dawo da El-Rufai domin cike wannan gibi.
A cewarsa, El-Rufai na da tasiri sosai a tsakanin masu ruwa da tsaki a Arewa maso Yamma, kuma hakan na iya taimaka wa APC wajen shawo kan ƙalubalen siyasa da ke tafe.
Maganar Nataro kan Rabiu Kwankwaso
Nataro ya ce ya kamata rade-radin da ke yawo kan yiwuwar Rabiu Musa Kwankwaso shiga sabuwar haɗaka a ƙarƙashin jam’iyyar ADC ya tayar da hankalin duk masu goyon bayan Shugaba Tinubu.
Ya ƙara da cewa ko da gwamnan Kano na yanzu, Abba Yusuf, ya shiga APC, hakan kaɗai ba zai wadatar wajen cike gibi a yankin ba.
A ra’ayinsa, akwai buƙatar mutum mai tasiri da kwarewa wajen tsara dabarun siyasa a Arewa maso Yamma, wanda ya ce El-Rufai ne ya fi dacewa da wannan rawar.

Source: Facebook
Nataro ya daura alhakin nesanta El-Rufai daga jikin Tinubu kan wasu ‘yan siyasa masu hassada da masu adawa cigabansa.
Tasirin dawowar El-Rufai ga Tinubu
Nataro ya ce akwai gagarumin aiki da ke gaban APC wajen tallata Shugaba Tinubu a Arewa maso Yamma kafin zaben 2027.
Daily Post ta wallafa cewa ya bayyana cewa El-Rufai na da kwarewa da ƙarfin hali da za su ba shi damar jagorantar wannan aiki cikin nasara.
APC ta yi magana kan nasarar Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar Kwara ya yi magana kan nasarar Mai girma Bola Ahmed Tinubu a babban zaben 2027.
Legit Hausa ta gano ya yi maganar ne yayin taron kaddamar da rajistar 'yan jam'iyyar ta yanar gizo wanda Abdullahi Ganduje ya fara yunkuri da yake ofis.
Shugaban na jam'iyya mai milki ya yaba wa gwamnan jihar Kwara kan yadda ya ke hada kai da gwamnatin tarayya wajen kawo cigaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

