Damagum: Wike Ya Fasa Kwai kan Shugaban Jam'iyyar PDP, Ya Yi Zarge Zargen Kudi

Damagum: Wike Ya Fasa Kwai kan Shugaban Jam'iyyar PDP, Ya Yi Zarge Zargen Kudi

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi raga-raga da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum
  • Wike ya zargi Damagum da kasance wa mutum mara kwarewa wanda bai san halin da jam'iyyar PDP take ciki ba
  • Ministan ya kuma kalubalanci shugaban na PDP da ya kai shi kotu idan har yana ganin maganganun da ya fada a kansa ba haka suke ba

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki shugaban jam’iyyar adawa ta PDP da ke cikin rikici, Ambasada Umar Damagum.

Wike ya bayyana Damagum a matsayin “mai karbar haraji” wanda bai da ladabi da nagartar da za su ba shi damar jagorantar jam’iyyar.

Wike ya soki shugaban PDP na kasa
Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum tare da Nyesom Wike Hoto: @OfficialPDPNig, @GovWike
Source: Facebook

Ministan ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Channels Tv a shirinsu na 'Politics Today'' da aka watsa da yammacin ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

"Bai da wani zabi": Wike ya gano dalilin Atiku na ficewa daga jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Wike ya ce kan Damagum?

Wike ya zargi Damagum da rashin kwarewa da sanin halin da ake ciki lokacin da PDP ta shiga rikicin shari’a, yana mai cewa shi ne da kansa ya shiga tsakani don daidaita jam’iyyar a lokacin.

“Damagum ma bai san waye lauyansa ba lokacin da muka shiga kotu. Haka muka dage muka iya tabbatar da daidaito kuma muka bar Damagum a mukaminsa."

- Nyesom Wike

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya kara da cewa Damagum mutum ne da ke gudanar da harkokinsa bisa son kudi kawai, ba tare da la’akari da amana ko ka’ida ba.

“Amma ka ga, kamar yadda yake, mai karbar haraji ne. Damagum mai karbar haraji ne. Bai bukatar aiki da FIRS, shi kamfanin karbar haraji ne."
“Wasu mutane haka suke da halinsu. Suna ganin kudi shi ne komai a rayuwa. Ba su da jajircewa ko tsayin daka a kan gaskiya."

Kara karanta wannan

Rikici ya tsananta: Zanga zanga ta barke a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja

- Nyesom Wike

Wike ya kalubalanci Shugaban PDP

Wike ya kuma kalubalanci Damagm da ya kai shi kotu idan yana ganin ya bata masa suna.

Wike ya yi kalamai masu kaushi kan Umar Damagun
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook
“Bari Damagum ya kalubalance ni. Ya kai ni kotu, ya ce, ‘Ga abin da minista ya fada kaina.’ Yasan ba zai iya yin hakan ba."

- Nyesom Wike

Maganganun Wike sun zo ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida a PDP ke kara kamari, inda bangarorin jam’iyyar biyu na Damagum da na Sanata Samuel Anyanwu, ke ci gaba da fafatawa kan ikon jagoranci a matakin kasa.

Wike ya fadi dalilin Atiku na barin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake taso da batun ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar daga jam'iyyar PDP.

Nyesom Wike ya bayyana cewa Atiku ya ga uwar bari ne shiyasa ya tattara komatsansa ya fice daga jam'iyyar PDP wadda ya yi takara karkashinta a zaben shejarar 2023.

Kara karanta wannan

Tsagin Wike ya mamaye sakatariyar PDP, an samu mukaddashin shugaban jam'iyya na kasa

Ministan ya kara da cewa Atiku ya rabu da PDP ne saboda ya san cewa ba zai iya cimma muradunsa a jam'iyyar ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng