Ya Bar PDP? Gaskiya Ta Fito game da 'Sauya Sheƙar' Tsohon Gwamnan Benue zuwa APC

Ya Bar PDP? Gaskiya Ta Fito game da 'Sauya Sheƙar' Tsohon Gwamnan Benue zuwa APC

  • Bede Bartholomew ya karyata jita-jitar cewa tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam ya sauya shema zuwa jam’iyyar APC
  • Jita-jitar komawar Sanata Suswam ta karade soshiyal midiya bayan da ya amsa gayyatar da Gwamna Hyacinth Alia ya yi masa
  • Sanata Suswam ya gode wa magoya bayansa, yana mai kira a gare su da su kwantar da hankali da ci gaba da goya masa baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue – Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Torwua Suswam ya warware rudanin da aka samu game da zargin ya koma jam'iyyar APC.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Bede Bartholomew, ya karyata rahotannin da ke yawo cewa Suswam ya bar PDP zuwa APC mai mulki.

Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam bai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ba
Tsohon gwamnan jihar Benue yana jawabi a wani taro. Hoto: Gabriel Torwua Suswam
Source: Facebook

Gaskiya kan sauya shekar tsohon gwamna

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, Bartholomew ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta karya ne kuma ba su da tushe, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Sanata Suswam yana nan daram a matsayinsa na ɗan siyasar da yake da cikakken tsari da kuma biyayya ga jam'iyyar da yake bi a halin yanzu.

Sai dai ya yarda cewa Gabriel Suswam ya amsa gayyatar gwamnan Benue, Hyacinth Alia, na halartar taron liyafa da aka shirya a gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi.

Sai dai ya ce wannan amsa gayyata tare da zuwa liyafar ba wai alama ce ko tabbaci na komawar tsohon gwamnan zuwa APC ba.

“Na samu kira daga mutane da dama suna tambaya ta game da labarin da ke yawo cewa Sanata Gabriel Suswam zai koma APC yau, kuma za a karɓe shi a gidan gwamnati da yamma."

- Bede Bartholomew

“Komawar Suswam APC jita-jita ce” - Bartholomew

Bartholomew ya ce babu gaskiya a wannan labari da ake yadawa, domin ba a ji daga bakin Sanata Suswam kai tsaye ko ofishin watsa labaransa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gwangwaje 'yar kabilar Igbo da kyautar ban mamaki a Borno

“Ina karyata wannan jita-jita da babbar murya saboda karya ce tsantsa wadda ba ta da wani asali. Ya kamata a yi watsi da ita gaba ɗaya,” in ji Bartholomew.

Hadimin tsohon gwamnan Benue ya kara da cewa gayyatar gwamnan ba ta da nasaba da siyasa ko sauya sheka.

Sanarwar ta kara da cewa:

“A matsayinsa na tsohon gwamna, Sanata Suswam yana daga cikin masu ruwa da tsaki a ci gaban jihar Benue, shi ya sa ya amsa gayyatar gwamnati. Babu wani abu da ya shafi siyasa a ciki.
A 2024 ne tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam ya nuna sha'awar neman shugabancin PDP
Hoton tambarin jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

An kwantar da hankalin magoya bayan Suswam

Mai tallafawa tsohon gwamnan ya bukaci magoya bayan Suswam da jama’ar jihar Benue da su yi watsi da jita-jitar sauya shekar.

Ya yi godiya ga wadanda suka rika kiran waya domin tabbatar da gaskiyar zancen, yana mai cewa Sanata Suswam yana godiya ga goyon baya da addu’o’insu.

An dakatar da Suswam daga PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rikicin cikin gida ya taba yin kamari a jam'iyyar PDP a jihar Benue da ke Arewa ta tsakiyan Najeriya a 2024.

Kara karanta wannan

Fiye da kwanaki 100 bayan rasuwarsa, an fara shiryen shiryen birne tsohon gwamna

Saboda rikicin, PDP ta sanar da dakatar da shugabannin kananan hukumomin Apa, Gboko, Gwer-East Katsina-Ala, Konhisha, Logo, Otukpo da Ukum.

Hakazalika, rahoto ya nuna cewa cikin wadanda aka dakatar akwai Sanata Gabriel Suswam, tsohon gwamnan jihar da Tergu Tsegba da Richard Gbande.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com