"Kun San Su": ADC Ta Bayyana Irin Mutanen da Za Ta Kawar daga Tsarin Siyasar Najeriya
- Sakataren jam’iyyar ADC na kasa, ya ce jam’iyyarsu za ta rushe tsarin siyasar ubangida da amfani da kudi
- Rauf Aregbesola ya ce ADC jam’iyya ce da Allah ya yi wa albarka domin ’yantar da talakawan Najeriya
- Tsohon gwamnan na jihar Osun ya bayyana yadda tsarin jam’iyyar ya bambanta da na kowace jam’iyya a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja – Sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola, ya yi magana kan sabon salon da za su kawo a siyasar Najeriya.
Rauf Aregbesola ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta yi niyyar kawar da tasirin ubangida, amfani da kudi daga tsarin siyasar kasar nan.

Source: Twitter
Sakataren na ADC ya bayyana hakan ne yayin wani taro da kungiyar 'Conscience Forum' ta shirya a ranar Lahadi, inda aka tarbi sababbin mambobi, cewar rahoton da jaridar TheCable ta kawo.
ADC ta bambanta da sauran jam'iyyu
Rauf Aregbesola ya bayyana cewa Allah ne ya kawo jam'iyyar ADC don ceton 'yan Najeriya.
"ADC ba jam’iyya bace irin sauran jam’iyyu a Najeriya. Mutane suna tunanin kamar sauran jam'iyyu take."
- Rauf Aregbesola
Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ADC jam'iyyar kare muradun jama'a ce, inda ya kara da cewa hakan ne ya bambanta ta da sauran jam'iyu.
"Babu wata jam'iyya da take da irin hakan a kundinta. Duk lokacin da wani ya yi magana kan akisa, ku gaya masa cewa ADC jam'iyya ce da Allah ya kawo don ceto Najeriya."
- Rauf Aregbesola
Mecece akidar jam'iyyar ADC?
Tsohon ministan harkokin cikin gidan ya bayyana cewa akidar ADC ita ce kafa gwamnati mai kula da jama’a.
"Akidar ADC ita ce gwamnati mai tausayi ga jama’a. Wannan shi ne babban burin jam’iyyar, bauta wa talakawa. Babu wata jam’iyya a Najeriya da ta sanya irin hakan a kundinta."

Kara karanta wannan
'Yan hadaka na shirin sauya jam'iyya daga ADC zuwa ADA,? An ji yadda lamarin yake
- Rauf Aregbesola
Ya kara da cewa ADC jam’iyya ce da ke karfafa muradun ma’aikata, masu sana’o’i, da talakawa gaba daya.
Aregbesola ya ce ADC za ta kawo sauyi
Rauf Aregbesola ya jaddada cewa jam’iyyar ADC za ta sake fasalin siyasar Najeriya domin hana mulkin mallaka daga hannun ’yan siyasa masu amfani da kudi.
“Kun san su, ni ma na san su. Muna yi musu bankwana. Bankwana da siyasar jaga-jaga. Muna yi musu bankwana su duka."
- Rauf Aregbesola

Source: Facebook
Karanta wasu karin labaran kan ADC
- 'Ba zai yiwu ba,' APC ta yi wa sakataren ADC martani kan kifar da Tinubu a 2027
- 'Za Mu Fitar da Tinubu daga Aso Rock Villa,' Aregbesola Ya Fadi Shirin ADC a 2027
- 'Za a kori shugabannin hadaka,' Kachikwu bai ganin David Mark zai rike ADC
ADC ta musanta batun komawa jam'iyyar ADA
A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren yada labaran jam'iyyar ADC na kasa, Bola Abdullahi, ya tsage biri har wutsiya kan jita-jitar 'yan hadaka za su koma jam'iyyar ADA.
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya kan rade-radin da ke cewa mambobin hadaka za su koma sabuwar jam'iyyar ADA, idan ta tsallake rajista.
Sakataren yada labaran ya nuna cewa jam'iyyar ADC ita ce ta 'yan hadaka, kuma za su ci gaba da zama a cikinta.
Asali: Legit.ng

