2027: ADA, ATP da Kungiyoyi 11 Sun Tsallake Tantancewar Zama Jam'iyyun Siyasa
- Hukumar INEC ta ce kungiyoyi 157 da ke neman rajista a matsayin jam’iyyun siyasa sun gaza tsallake tantancewar farko
- INEC ta ce kungiyoyi 14 kacal ne suka tsallake matakin farko na tantancewar, kuma za ta gana da su ranar 17 ga Satumba, 2027
- Yayin da hukumar ta fadi matakin da za ta dauka na gaba, ta lissafa kungiyoyin 14 da suka hada da ADA, AAP, ATP da sauransu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar INEC ta sanar da cewa kungiyoyi 157 da suka nemi zama jam’iyyun siyasa sun gaza tsallake matakin farko na tantancewa, inda aka yi fatali da bukatunsu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, ta kara da cewa akwai kungiyoyi 14 da suka tsallake wannan mataki, kuma yanzu haka ana duba bukatunsu.

Source: Getty Images
INEC ta bayana hakan ne a cikin sanarwar da mai magana da yawunta, Sam Olumekun ya fitar a shafin hukumar na X, a ranar Alhamis, 11 ga Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyi 157 sun fadi jarabawar zama jam'iyyu
Sam Olumekun, ya bayyana cewa wannan hukunci ya biyo bayan rahoton kwamitin da ke duba bukatun rajistar sababbin jam'iyyun siyasa.
A cewarsa, INEC ta karɓi bukatu 171 gaba ɗaya, inda kowanne aka tantance shi bisa tanade-tanaden Sashe na 222 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da kuma Sashe na 79 na Dokar Zabe ta 2022, da ƙa’idojin hukumar na shekarar 2022.
"Daga cikin wannan adadi, kungiyoyi 14 ne kawai suka cika sharuda na tsallakewa zuwa mataki na gaba, yayin da kungiyoyi 157 suka gaza tsallakewa.
"Hukumar za ta aika sako ga dukkan kungiyoyin da abin ya shafa dangane da matakin da ta dauka a wannan taro, cikin awanni 24."

Kara karanta wannan
Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba
- Sam Olumekun.
Matakin INEC na gaba kan kungiyoyin 14
Olumekun ya ce za a gayyaci shugabanni da sakatarorin wucin-gadi na kungiyoyin da suka tsallake tantancewar farko zuwa taro a ofishin INEC da ke Abuja.
Sanarwar ta ce za a gudanar da wannan taro a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Hukumar ta bukaci wadannan kungiyoyi su dora wasu bayanai a dandalin yanar gizon INEC, sannan za ta gudanar da tantancewar zahiri kan dukkan bayanan da kungiyoyin suka gabatar.
“Bayan wannan mataki ne za a yanke shawara ta karshe kan cancantar kowace kungiya ta zama jam’iyyar siyasa bisa bin ka’idojin doka."
- Sam Olumekun.
INEC ta kara da cewa rajistar jam’iyyu aiki ne da yake gudana a bisa doka, kuma hukumar za ta ci gaba da karbar sababbin bukatu daga kowace kungiya da ta cika sharuddan da doka ta tanada.

Source: Twitter
Kungiyoyi 14 da suka tsallake tantancewar INEC
Ga sunayen kungiyoyin da suka samu nasarar tsallake matakin farko na tantancewa:
- African Transformation Party (ATP)
- All Democratic Alliance (ADA)
- Advance Nigeria Congress (ANC)
- Abundance Social Party (ASP)
- African Alliance Party (AAP)
- Citizens Democratic Alliance (CDA)
- Democratic Leadership Alliance (DLA)
- Grassroots Initiative Party (GRIP)
- Green Future Party (GFP)
- Liberation People’s Party (LPP)
- National Democratic Party (NDP)
- National Reform Party (NRP)
- Patriotic Peoples Alliance (PPA)
- Peoples Freedom Party (PFP)
''Yan siyasa na kamfe a sakaye' - INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar INEC ta bayyana damuwa kan yadda wasu 'yan siyasa suka fara jirkita mata lissafin zaben 2027.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban hukumar TEI, Farfesa Abdullahi Zuru, ya ce yanzu haka wasu 'yan siyasa na yakin neman zabe a fakaice.
Farfesa Zuru ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su mutunta tsarin doka da ka’idojin da aka shimfida domin kare ingancin tsarin dimokuradiyya a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
