Jam'iyyun Siyasa 5 Sun Hadu don Taimaka wa ADC a Kifar da Gwamnatin APC a 2027
- Shirin kifar da gwamnatin APC ya kankama yayin da jam'iyyun adawa, da suka hada da PDP, LP, da wani tsagi na APC sun haɗa kai
- An ce jam'iyyun sun yanke shawarar yin takarar zaben fitar da gwani a ƙarƙashin jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, don kafa gwamnati
- Shugabannin gamayyar sun ce za su yi amfani da dabarun siyasa na dimokuraɗiyya don jan ra'ayin 'yan Najeriya a zaben mai zuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ebonyi - Gabanin zaɓen 2027, shugabannin jam'iyyun adawa a jihar Ebonyi sun haɗa kai don marawa jam'iyyar ADC baya.
Wannan gamayya ta ƙunshi shugabannin jam’iyyu, da suka hada da PDP, LP, APGA, YPP da wani tsagi na jam'iyyar APC.

Source: Facebook
2027: Jam'iyyun sun shiga hadakar ADC
A taron farko da suka gudanar a Abakaliki a ranar Lahadi, shugabannin sun yi alƙawarin karɓar mulki a jihar a zaɓen 2027, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wurin taron, tsohon ɗan takarar sanata na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Chief Linus Okorie, ya bayyana kwarin gwiwar cewa ADC za ta mulki Najeriya daga shekarar 2027.
Cif Linus Okorie ya ce, sun fahimci cewa manufar jam'iyyar ADC ita ce faɗaɗa cigaban Najeriya ta hanyar dimokuraɗiyya.
A cewarsa, shugabannin jam'iyyun adawa sun haɗu ne don kafa kawance mai ƙarfi da nufin yin aiki tare da 'yan Najeriya don cimma burinsu.
"Jam'iyyar ADC za ta mulki Najeriya" - Linus
Tsohon dan takarar ya ce:
“Mun hadu ne domin mu ceto Najeriya daga halin da take ciki ta hanyar demokaraɗiyya. Ba mu haɗu don mu taka wa wani mutum ko jam'iyya ba, kuma ba za mu ci mutuncin kowa ba. Mun haɗu ne don mu tattauna yadda za mu hada kai da 'yan Najeriya a kawo sauyi a kasa.
"ADC za ta mulki Najeriya da yardar Allah da kuma goyon bayan kowa da kowa. Wannan ya sa mu ka hadu a nan daga garuruwa da jam'iyyu daban daban, don tsara yadda hakan za ta kasance."
Ya ƙara da cewa za a ware wata rana ta musamman don kaddamar da ADC a jihar, kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da su ci gaba da yin aiki tuƙuru don tabbatar da nasararta a babban zaɓen 2027.

Source: Original
'ADC na samun goyon baya' - Misis Jenifer
Jaridar Vanguard ta rahoto shugabar ADC a jihar, Misis Jenifer Adibe, ta ce jam’iyyarta na samun goyon baya daga mazauna jihar saboda muradinta na yin tafiya da kowa.
“ADC jam’iyya ce da aka kafa ta kan riƙon amana. Mun jajirce wajen tabbatar da gaskiya da shugabanci na gari. Za mu tabbatar cewa muna da magoya baya masu yawa a jihar.
"ADC a jihar Ebonyi za ta samar da kuri’u akalla miliyan 3 a babban zaɓen 2027, kuma mun shirya ganin cewa hakan ta tabbata."
- Misis Jenifer Adibe.
Manyan 'yan siyasa sun shiga ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu fitattun 'yan siyasar Najeriya, sun fice daga jam'iyyunsu daban daban, zuwa hadakar 'yan adawa a karkashin ADC.
Baya ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da Nasir El-Rufai, da ke jagorantar 'yan adawa, an samu wasu manyan 'yan siyasa sama da 20 da suka shiga ADC.
Wasu daga cikin manyan kasar da suka shiga ADC sun hada da David Mark (tsohon shugaban majalisar dattawa), Abubakar Malami (tsohon ministan shari'a), da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

