Ina Makomar Tinubu?: APC Ta Ce Za Ta ba Kowa Dama Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa
- Ba lallai ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu tikitin tsaya wa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC kai tsaye ba
- APC ta fito ta bayyana cewa ba za ta rufe kofa ga 'yan jam'iyyar da ke son tsaya wa takarar shugaban kasa a karkashinta ba
- Wannan na zuwa ne bayan kwamitin APC na kasa (NWC), gwamnoni, rassan jam'iyyar na jihohi sun amince da tazarcen Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta musanta jita-jitar cewa za ta fitar da fom din neman takarar shugaban ƙasa guda ɗaya kacal a 2027.
Yayin da APC ta nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu, jam'iyyar ta ce ba za ta hana jiga-jigan jam’iyya tsayawa takara zaben fitar da gwani ba.

Source: Twitter
Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Sulaiman Argungu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta tabbatar da goyon baya ga Tinubu
Argungu ya tabbatar da cewa kwamitin aiki na ƙasa (NWC) da kuma rassan jam’iyyar a jihohi sun amince da Tinubu a matsayin dan takara daya tilo a 2027, amma ya jaddada cewa har yanzu kofar takara a buɗe take ga kowa.
Sakataren ya ce:
“Mu a NWC mun riga mun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa a 2027. Haka ma sauran sassa na jam’iyyar suka yi
“Gwamnoni a jihohi suma sun bi sahu, kuma an tabbatar da hakan a dukkan yankunan ƙasar guda shida. Amma hakan ba yana nufin an rufe kofa ga masu son yin takara ba”
'Kofar takara a bude take a 2027'- APC
Alhaji Sulaiman Argungu ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan
'APC da PDP sun tafka kuskure, da yiwuwar su sha kaye a zaben shugaban kasa na 2027'
“Idan lokacin da ya yi, za mu fitar da jadawalinmu. Ba za a hana duk wanda ke son tsayawa takarar shugaban ƙasa a karkashin APC damar sayen fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara ba.
“Ba mu taɓa cewa mun rufe kofa ba. Abin da muke yi kawai shi ne yaba abin da shugaban ƙasa yake yi wa ‘yan ƙasa, shi ya sa muka amince ya nemi wa’adi na biyu.
“Dimokuraɗiyya ba ta amince da mulkin kama-karya ba. Duk da yawancinmu mun amince da Tinubu, duk wani ɗan jam’iyya da ke son tsayawa takara a APC zai samu wannan dama."

Source: Twitter
APC ta bambanta kanta da jam'iyyar PDP
Rahton Vaonguard ya nuna cewa matsayar APC ta sha bamban da abin da jam’iyyar PDP ta yi a shekarar 2014 lokacin da ta buga fom ɗaya tak na tsayawa takarar shugaban ƙasa ga Goodluck Jonathan.
"A shekarar 2014, PDP ta buga fom ɗaya ne kacal na neman tsayawa takarar shugaban ƙasa ga Jonathan, inda hakan ya hana sauran jiga-jigai damar tsayawa takara.
"Sai dai, APC ta bayyana kanta a matsayin jam’iyyar dimokuraɗiyya wadda ke bai wa mambobinta damar nuna bajintarsu."
-Alhaji Sulaiman Argungu.
Gwamnonin APC sun tsaya bayan Tinubu
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnonin APC mai mulki a Najeriya sun gamsu da kamun ludayin shugabancin mai girma Bola Tinubu.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma ya gabatar da ƙudiri domin a amince Bola Tinubu ya zama ɗan takara a 2027.
Ƙudirin nasa ya samu amincewar dukkanin mahalarta taron ƙoli na jam'iyyar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

