Gudaji Kazaure da Manyan Ƴan Siyasa 7 da Suka Hango Faduwar Tinubu da APC a 2027
Abuja - Yanzu hankula sun koma ne kan zaɓen 2027 a Najeriya, kuma kamar yadda aka saba, ‘yan siyasa na ta ƙoƙarin yin duk abin da zai tabbatar musu da nasara.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A gabanin 2027, shirin kifar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki ta hanyar zaɓe yana ƙara karfi, inda wasu ‘yan siyasa takwas suka yi hasashen faduwarsa.

Source: Twitter
Masu ganin Bola Tinubu ya fadi zabe
Legit.ng ta kawo muku jerin fitattun ‘yan siyasa takwas da suka yi hasashen faduwar Tinubu a zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Gudaji Muhammadu Kazaure
A watan Yuli, 2025, tsohon ɗan majalisar wakilai, Muhammad Kazaure, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai sha kasa a zaɓen 2027 tun kafin karfe 12:00 na rana.
Gudaji Kazaure ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da AIT ta wallafa wanda ya karafe kafofin sadarwa.

Kara karanta wannan
ADC: An samu wanda zai dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a 2027
"Ina da tabbaci zuwa karfe 12:00 na rana, Asiwaju ya sha kasa, wannan shi ne kwarin gwiwarmu."
- Hon. Gudaji Kazaure.
Kalli bidiyon a kasa:
2. Solomon Dalung
Solomon Dalung, tsohon ministan wasanni da ci gaban matasa, ya ce ya riga ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa gwamnatinsa za ta fadi a 2027, ko da kuwa ɗansa, Seyi Tinubu, aka naɗa shugaban hukumar INEC.
Dalung ya bayyana hakan a hirarsa da News Central a watan Yulin 2025, inda ya shaida cewa gwamnatin Tinubu ta yi fito na fito da talakan Najeriya, tare da mayar da talauci makami.
'Dan adawar ya taba cewa Tinubu ne shugaban Najeriya tilo da ya bayyana karara cewa yana ƙin talakawa ta hanyar jefa su a talauci da wahala, kamar yadda muka ruwaito.
3. Dabo Sambo
A watan Yuni, 2025 dattijon Arewa kuma mai sharhi kan harkokin jama’a, Alhaji Dabo Sambo, ya roƙi Shugaba Tinubu da ya magance matsalar rashin tsaro da ta’addanci a Arewa cikin gaggawa.
Alhaji Dabo Sambo ya gargadi Tinubu cewa rashin yin hakan zai iya rage masa damar sake lashe zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
Mun ruwaito dattijon ya bayyana cewa:
“Idan Shugaba Tinubu ya ƙi kawar da matsalar tsaro, tabbas ba zai lashe zaɓen 2027 ba.”
4. Datti Baba-Ahmed
A watan Afrilu, 2025 Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, ya ba da shawara ga Tinubu da kada ya sake ya nemi wa’adi na biyu, idan yana so a kira shi ɗan siyasa mai basira.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan a shirin siyasa na Arise TV, yana mai cewa lokaci ya kure wa Tinubu da jam’iyyarsa ta APC, saboda alamu sun nuna faduwarsu a 2027.
5. Shehu Gabam
A watan Maris, 2025, jagoran jam’iyyar SDP, Shehu Gabam, ya ce ko wane mutum na iya faduwa zaɓe a 2027, ciki har da Shugaba Tinubu.
Ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsa ta SDP ce za ta lashe zaɓen, domin gwamnatin da ke mulki yanzu ba ta sauraron koke-koken ‘yan Najeriya.
6. Adewole Adebayo
A watan Maris, 2025 Adewole Adebayo, ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a 2023, ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu zai sha kasa a 2027.
Adewole Adebayo ya ce:
“Za a cire Tinubu daga mulki, wannan abu ne tabbatacce, kuma shugaban ƙasa na gaba zai fito ne daga SDP."
7. Charles Udeogaranya
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Charles Udeogaranya, ya ce jam’iyyar APC za ta sha kaye idan ta tsayar da Tinubu a matsayin ɗan takara a 2027.
Charles Udeogaranya ya ce:
“A ganina da yawancin ‘yan Najeriya, ya gaza warware matsalolin ƙasa. Babban kuskure shi ne sake tsayar da shi, amma Allah ya hana.”

Source: Twitter
8. Nasir El-Rufai
A watan Yuni, 2027, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce sake lashe zaɓe ga Shugaba Tinubu a 2027 abu ne mai matukar wahala.
Ya ce a wata hira da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, El-Rufai ya ce, “duk wanda yake tunanin hakan za ta yi wu, to bai san halin da Najeriya take ciki ba.”
El-Rufai ya ce ‘yan Najeriya sun riga sun dawo daga rakiyar Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC, don haka ba za su sake zaɓar su a 2027 ba.

Kara karanta wannan
Malamin addini ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu, ya fadi sharadin da zai sa ya sha kaye
Malami ya hango faduwar Tinubu a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani malamin gargajiya da ya yi hasashen nasarar APC a 2023, yanzu ya hango faduwar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
A wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga malamin yana kulumboto, tare da cewa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben mai zuwa.
Hasashen malamin dubar ya jawo cece-kuce, yayin da 'yan Najeriya suka zura ido suka ko hasashensa zai zama gaskiyar kamar na baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
