Yadda PDP ke Kai Kawo wajen Lalubo Wanda Zai Gwabza da Tinubu a Zaben 2027
Abuja - Jam'iyyar adawa, PDP ta fara laluben sanannen ɗan siyasar da za ta tsaida takarar shugaban kasa, wanda zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
PDP ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki da shugabanninta domin jin ra'ayoyinsu kan batun wanda ya dace ya kare martabar jam'iyya a zaɓe na gaba.

Asali: Facebook
The Nation ta tattaro cewa hakan ya biyo bayan matakin da kwamitin zartarwa na PDP (NEC) da ƙungiyar waɗanda suka kafa PDP suka ɗauka na bai wa Kudu takara.
Kai ya fara rabuwa a PDP kan takarar Kudu
Sai dai wannan tsari na ware tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP ga Kudu bai yi wa wasu ƴan jam’iyyar daɗi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata ƙungiya mai suna Gbenga Hashim Solidarity Movement ta bayyana cewa babu wani, "sahihin ɓangaren shugabancin PDP da ya yanke shawarar miƙa takara ga Kudu."

Kara karanta wannan
YouthCred: Gwamnatin Tinubu ta kawo shirin da kowane matashi zai iya samun N200,000
Ƙungiyar na goyon bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim, wanda ya fito daga Arewa ta Tsakiya.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Abdulrazaq Hamzat, a cikin wata sanarwa, ya ce ko da an tattauna ta bayan fage, waɗanda suka yanke wannan hukunci ba su da ikon yin haka a doka.
Ya yi fatali da furucin Farfesa Jerry Gana cewa shugabannin PDP na jihohin Arewa sun amince baki ɗaya da a ɗauko ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar daga kudu.
2027: Jiga-jigai 5 da PDP ta fara nazari kansu
Sai dai yayin da aka fara kai ruwa da rana kan batun yankin da za a miƙa takara, shugabannin PDP da masu ruwa da tsaki sun fara faɗar ra'ayoyinsu.
An ruwaito cewa sunayen jiga-jigai biyar sun bayyana, ana ganin sune a sahun gaba duba da tasirinsu a siyasa da kuma ƙarfin magoya bayansu. Ga su kamar haka:

Kara karanta wannan
Tinubu na tsaka mai wuya, PDP ta fara nuna wanda za ta tsayar takara a zaɓen 2027
1. Dr. Goodluck Jonathan
Majiyoyi sun bayyana wani gwamnan Arewa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan shirin dawo da Goodluck Jonathan takarar shugaban ƙasa.
The Cable ta rahoto cewa gwamnan ya taɓa zama minista a ƙarƙashin gwamnatin Jonathan, kuma zai so ya zama abokin takararsa a 2027.
Lissafin gwamnan shi ne samun damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2031 idan Jonathan ya yi nasara a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Sai dai majiyoyin sun ce wannan shirin na iya fuskantar cikas saboda Sashe na 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).
Sashen dokar ya haramta wa duk wanda aka rantsar sau biyu a matsayin shugaban ƙasa sake tsayawa takara.
Wannan sashen na doka ya ce:
“Mutum da aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa domin kammala wa’adin wani da aka zaɓa, ba zai sake neman zaɓen wannan kujera fiye da sau ɗaya ba.”

Kara karanta wannan
Bayan ya baro PDP, Sanata Melaye ya kawo hanyar da ADC za ta buga Tinubu da ƙasa a 2027
Wannan doka ta shiga kundin tsarin mulkin Najeriya ne bayan shugaban lasa, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a ranar 11 ga watan Yuli, 2018.
Hakan ya yasa masana suka kai ruwa rana kan ko dokar za ta zaman tarnaki ga wadanda suka rike mukamin shugaban kasa kafin 2018 kamar Jonathan.
Wasu ke ganin tun da gyara ne na doka zai hau kan kowa amma wasu masana sun ce sashen dokar bai yi bayani karara cewa zai shafi kowa ba.
Don haka a cewar wasu masana doka za a dauka sashen dokar ya fara aiki ne a 2018, ba zai kawo cikas ga wadanda suka rike kujerar shugabanci kafin lokacin ba kamar Jonathan wanda ya sauka mulki a 2015.
Watanni biyu da suka wuce, tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Patience Jonathan, ta ba da alamar cewa mijinta ba zai tsaya takara a 2027 ba, rahoton This Day.
A wani bikin bayar da lambar yabo da aka gudanar a Abuja, Dame Patience ta bayyana goyon bayan danginta ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
2. Nyesom Wike
Mambobin PDP da ke goyon bayan Wike suna ambato irin gudummawar da ya bayar ga jam’iyyar tsawon shekaru da kuma yadda yake da tasirin siyasa a faɗin jihohi 36.
Wani ɗan majalisar tarayya da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
"Wike ya sadaukar da lokaci da dukiyarsa sosai wajen riƙe PDP, kuma ba don ƙoƙarinsa ba, wasu daga cikinn shugabannin jam'iyyar na yanzu ba za su kai ko'ina ba.

Asali: Facebook
Sai dai a rahoton BBC News, ministan harkokin Abuja da kansa ya riga ya bayyana cewa ba shi da sha’awar tsayawa takara ya gwabza da Shugaba Tinubu.
Majiyoyi sun kuma ce ba zai yiwu Nyesom Wike ya shiga takara da tsohon ubangidansa Goodluck Jonathan ba idan har tsohon shugaban ƙasar ya amince zai yi takara.
3. Mista Peter Obi
Wasu shugabannin PDP na ƙoƙarin jawo Peter Obi ya koma jam’iyyar, domin zai taimaka wajen ceto jam'iyyar daga rushewa baki ɗaya sakamakon yadda ƴan siyasa ke sauya sheƙa.
Sun kawo sunansa ne saboda yadda ya ba da mamaki a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu nasara.
A wani shirin Channels tv, Farfasa Jerry Gana, ya ce Obi na da duk abin da ake buƙata wajen kayar da kowanne ɗan takara a jihohin Arewa idan ya tsaya a ƙarƙashin PDP.

Asali: Twitter
Jerry Gana, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP ya ce:
"Ni mai bincike ne, kuma ina tattara ra’ayoyi. A jihohin Arewa, Peter Obi zai iya kayar da duk wani ɗan takara idan ya dawo PDP, domin mutanenmu masu adalci ne sosai."
Sai dai wasu mambobin PDP ba su yarda da alkawarin da tsohon gwamnan Jihar Anambra ya yi ba cewa zai yi wa’adi ɗaya kacal idan aka zaɓe shi.
4. Gwamna Seyi Makinde
Magoya bayan Gwamna Makinde na ganin cewa yana da damar fuskantar Shugaba Tinubu domin dukkansu ‘yan yanki ɗaya ne watau Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan
ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka
Hasashensu shi ne gwamnan zai iya raba ƙuri’un yankin, wanɗa a ganinsi hakan zai iya ba jam’iyyar PDP damar samun nasara a zaɓen 2027.
Wata majiya ta ce:
"A Kudu maso Yamma, gwamna guda ɗaya ne kawai ya rage na PDP da yake biyayya. Abokin aikinsa na Osun ma ya riga ya nuna goyon baya ga Tinubu a 2027.”
"Ana ci gaba da tattaunawa, kuma idan PDP ta takaita a wani yankin, misali Kudu maso Yamma, to gwamnan Oyo ne zai zama ɗan takara.”

Asali: Facebook
A watan Afrilu, Gwamna Makinde, a yayin da yake magana kan halin da ƙasar ke ciki, ya ce yana da ƙwarewa da gogewar shugabancin ƙasa, in ji rahoton Bussiness Day.
Makinde ya ce:
"Babu tantama na cancanta kuma ina da gogewar hawa kujera lamba ɗaya, ina da duk abin da ake bukata,"
"Amma a yanzu na maida hankali ne kan kokarin sauke nauyin jama'a, nauyin shugabanci da al'ummar Oyo suka ɗora mani."
5. Bukola Saraki
‘Yan jam’iyyar PDP masu goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki na ganin cewa ya kamata a saka masa lada saboda ya nuna wa PDP halacci.
A ganinsu Saraki ya zauna a PDP duk da halin da take ciki, bai yarda abokansa kamar tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya koma ADC, sun ruɗe shi ba.

Asali: Facebook
Haka kuma sun nuna cewa yana da abokai masu kuɗi waɗanda ba za su ji ƙyashin tallafa masa ba.
A ɗaya ɓangaren kuma, masu adawa da shi suna tambayar, wane yanki zai ce ya fito daga ciki, Arewa ko Kudu? Duba da matsayar da aka cimmawa na ba Kudu takara.
A cewar jiga-jigan PDP da ke adawa da takarar Saraki, bai kamata a ba tsohon sanatan takara ba saboda ɗan Arewa ne matuƙar ana son yin adalci a jam'iyyar.
A kwanakin baya, jam'iyyar PDP ta naɗa Bukola Saraki a matsayin shugaban kwamitin sulhu, kuma tun daga lokacin yake faɗi tashin lalubo hanyar warware rikicin jam'iyyar, kamar yadda Punch ta rahoto.
Sule Lamido na so PDP ta tsaida Jonathan
A wani rahoton, kun ji cewa Sule Lamido ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonthan ne mafi dacewa da tikitin PDP a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya shawarci jam'iyyar PDP da ta yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan domin ya dawo ya karɓi takara.
A cewarsa, Jonathan shi ne mafi dacewa a PDP a 2027 saboda ya taɓa shugabanci, ya fahimci yadda gwamnati take, kuma zai iya aiki da kowa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng