Wata Sabuwa: Ɗan Majalisar Wakilai Ya Bi Sahun Atiku, Ya Fice daga Jam'iyyar PDP
- Marcus I. Onobun, dan majalisar wakilai daga Edo, ya yi murabus daga PDP saboda rikicin cikin gida da rashin daidaito a cikin jam’iyyar
- A cikin wasiƙar da ya aike wa shugaban PDP na mazabarsa, Onobun ya bayyana cewa matsalolin jam’iyyar sun wuce a iya gyara su
- Yayin da ake jiran a ji jam'iyyar da zai shiga a nan gaba, dan majalisar wakilan ya gode wa PDP da al’ummarsa bisa goyon bayansu gare shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo — PDP ta yi babban rashi a Edo bayan Marcus I. Onobun, dan majalisar wakilai na mazabar Esan ta Yamma/Esan ta Tsakiya/Igueben ya ajiye mukaminsa daga jam’iyyar.
Murabus din dan majalisar wakilan na kunshe a cikin wasiƙar da ya aikewa shugaban PDP na mazabar Ward 6 a karamar hukumar Esan ta Yamma.

Source: Facebook
'Dan majalisar Edo ya fice daga PDP
A shafinsa na Facebook, Onobun ya bayyana cewa rikicin cikin gida, rashin daidaito a shugabanci, da sabanin da ba a shawo kansu ne suka sanya shi barin PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasikar da ya rubuta a ranar Alhamis, 18 ga Yuli, 2025, dan majalisar wakilan ya ce:
“A wannan lokaci na yanke shawara bayan tunani mai zurfi da kuma tuntuɓar shugabanni, abokan siyasa da al’umma ta.
"Ya bayyana a fili cewa matsalolin cikin gida, rikicin shugabanci da sabani da suka dabaibaye jam’iyyar sun kai matakin da ba za a iya warware su ba."
Onobun, wanda ya taɓa riƙe kujerar shugaban majalisar Edo, ya ce duk da cewa PDP ta taka muhimmiyar rawa a tafiyarsa ta siyasa, lokaci ya yi da zai tsaya tsayin daka kan muradunsa na ci gaba, haɗin kai da shugabanci nagari.
Onobun ya magantu kan jam'iyyar da zai shiga
A cikin sanarwa da ya fitar ga jama’a, Onobun ya ce:
“Yau na miƙa takardar murabus dina daga jam’iyyar PDP, wata kafa da na yi amfani da ita wajen hidima wa mutanena da kuma gina ƙasa.
"Wannan ba sauƙaƙƙen hukunci ba ne, amma bayan dogon tunani da tuntuɓar shugabanni, magoya baya da al’ummar Esan ya Yamma, Esan Tsakiya da Igueben, na yanke shawarar ɗaukar sabuwar hanya domin cimma burina na kawo ci gaba, daidaito da wakilci nagari.”
Ya sake tabbatar da cewa yana da niyyar ci gaba da yin hidima ga mutanensa, inda ya bayyana cewa tattaunawa na ci gaba domin sanar da jam'iyyar da zai shiga nan gaba.

Source: Twitter
'Dan majalisar ya yi wa PDP godiya
Duk da cewa Rt. Hon. Onobun bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba tukuna, ficewarsa ta ƙara yawan manyan jiga-jigan PDP da ke ficewa daga jam’iyyar musamman yayin da zaɓen gwamna na Edo ke ƙaratowa.
Dan majalisar dai ya yi godiya ga PDP bisa damar da jam’iyyar ta ba shi da kuma goyon bayan al’ummar mazabarsa tsawon shekarun da suka gabata.
"Duk da na ba da gudunmawa sosai a gina PDP, amma lokaci ya yi da zan dauki wannan babbar matsayar, domin nemawa al'ummata hanya mafi sauki ta amfanuwa da wakilci na."
- Marcus I. Onobun.
Karanta wasikar a nan kasa:
Hon. Marcus Onobun ya yi hatsarin mota
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan majalisar wakilai na mazabar Esan ta Yamma/Esan ta Tsakiya /Igueben a jihar Edo, Marcus Onobun, ya gamu da hatsarin mota a hanyar Abuja.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Edo, Tony Aziegbemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa dan majalisar ya samu raunuka a jikinsa.
A cewar sakataren watsa labaran Marcus Onobun, ɗan majalisar ba ya cikin wani mawuyacin hali da zai jawo damuwa, kuma yana samun kulawa ta likita yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


