Mambobin majalisa biyu sun yi murabus daga APC, sun koma PDP

Mambobin majalisa biyu sun yi murabus daga APC, sun koma PDP

- Wasu mambobin majalisar dokoki biyu a jihar Edo sun yi murabus daga jam'iyyar PDP tare da komawa PDP

- Marcus Onobun, kakakin majalisa, ya karanta wasikar murabus din APC a zauren majalisar da ke babban birnin Benin

- Gabanin zaben gwamnan Edo ne gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP daga APC

Wasu yan majalisu a majalisar dokoki ta jihar Edo da ke karkashin jam'iyyar APC sun rubuta takardar ficewa daga jam'iyyar tare da komawa jam'iyyar adawa ta PDP.

Yan majalisar guda biyu sune tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar kuma mamba mai wakiltar Akoko-Edo 1, Mr. Yekini Idaiye da kuma mamba mai wakiltar Orhionmwon ta Gabas, Mr. Nosayaba Plumber.

Kakakin majalisar, Marcus Onobun ya karanta wasikar murabus dinsu daga APC a zauren majalisar da ke babban birnin jihar, Benin, a ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Takardar murabus din Yekini na cewa: "Zan yi amfani da wannan dama domin sanar da ku murabus dina daga jam'iyyar APC.

KARANTA: 2023: Wasu gwamnonin APC huɗu sun matsa wajen zawarcin Jonathan domin yi wa jam'iyyarsu takara

"Na yanke wannan shawarar ne biyo bayan rikicin cikin gida na jam'iyyar a gunduma ta zuwa karamar hukuma, har ta kai ga an raba shugabancin jam'iyyar gida biyu."

Mambobin majalisa biyu sun yi murabus daga APC, sun koma PDP
Mambobin majalisa biyu sun yi murabus daga APC, sun koma PDP
Asali: Twitter

Wasikar murabus din Nosayaba Okunbor na cewa: "ina mai sanar da ku cewa na yanke shawarar barin jam'iyyar APC.

"Wannan ya biyo bayan matsalolin da ake ci gaba da samu ba tare da sanin ranar karewa ba.

KARANTA: Na barku da Allah akan zargin da kuke min; Obasanjo ya waiwayi tarihin marigayi Yar'adua

"Kuma na yi iya bakin kokari na don dinke barakar da ke a cikin jam'iyyar amma hakan ya ci tura, sakamakon wasu shuwagabannin jam'iyyar da ba son kawo karshen rikicin."

Onobun ya yi wa yan majalisun biyu maraba da zuwa jam'iyyar PDP tare da jinjina masu bisa kudirin yin aiki tare da Gwamnan jihar don kawo ci gaba mai dorewa a Edo.

Sauya shekar yan majalisun biyu ya sanya yanzu adadin mambobin majalisar a karkashin PDP ya koma tara, inda APC ke da mamba daya tal a majalisar dokoki ta jihar.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa Obasanjo ya yi Allah ya isa yayin da ya ke bayyana cewa yana da masaniyar cewa marigayi Umaru Musa Yar'adua bashi da koshin lafiya kafin ya goyi bayansa.

Tsohon shugaban kasar ya musanta zargin cewa kutunguila da kitimurmura suka sanya shi bawa Yar'adua takara a 2007.

Obasanjo ya jingine manyan 'yan siyasa da suka hada da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, da mataimakinsa a wancan lokacin, Atiku Abubakar, tare da goyawa Yar'adua baya wajen samun tikitin takara a jam'iyyar PDP.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel