Da duminsa: Kakakin majalisar jihar Edo da wasu 'yan majalisa 6 sun koma PDP

Da duminsa: Kakakin majalisar jihar Edo da wasu 'yan majalisa 6 sun koma PDP

- Kakakin majalisar jihar Edo, Rt. Hon. Frank Abumere Okiye ya koma jam'iyyar PDP

- Ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai ci ta PDP, tare da wasu 'yan majalisar jiha shida

- Bayan Okiye ya bayyana sauya shekar tasa yace an turo masa da wasiku 6 na sauya jam'iyya

Kakakin majalisar jihar Edo, Rt. Hon. Frank Abumere Okiye da wasu 'yan majalisar jihar sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba.

Sun bar jam'iyyar adawa ta APC zuwa jam'iyya mai ci ta PDP. Bayan Okiye ya sanar da sauya jam'iyyarsa, ya ce an turo masa wasiku 6 na sauya jam'iyya.

Sun ce sun sauya jam'iyya ne don su nuna yadda suke biye da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Kakakin ya ce rabuwar kan 'yan jam'iyyar APC na jihar Edo ne babban dalilin da yasa suka koma jam'iyyar PDP, don su samu damar wakiltar mazabunsu yadda ya dace.

Yanzu haka Gwamna Obaseki na da 'yan majalisar jiha 7 a jam'iyyarsa.

Wadanda suka sanar da sauya shekar tasu sun hada da Rt. Hon Frank Okiye, Hon. Asoro Osadebamwen Roland, Hon. Aluebhosele Ephraim, Hon. Ojiezele Osezua Sunday, Hon. Okhuarobot Henry, Hon. Okoduwa Emma da Hon. Marcus Onobun.

KU KARANTA: Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa (Hotuna)

Da duminsa: Kakakin majalisar jihar Edo da wasu 'yan majalisa 6 sun koma PDP
Da duminsa: Kakakin majalisar jihar Edo da wasu 'yan majalisa 6 sun koma PDP. Hoto daga Gov Obaseki
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abubuwa 13 da yakamata ku sani game da karin albashin malaman makaranta

Idan ba'a manta ba, an zabi dukkan 'yan majalisar jihar Edo 24 daga jam'iyyar APC. Sai dai, anyi ta rikici ta kai ga 'yan majalisa 9 ne kadai aka rantsar a 17 ga watan Yuni 2019.

Sauran 17 din a wasu wurare na daban aka rantsar da su na babban birnin jihar Benin.

A wani labari na daban, Sanata Smart Adeyemi, sanatan dake wakiltar Kogi ta yamma, ya sanar da niyyarsa ta amince da mika dokar yankewa barawo hannu don kawar da rashawa a Najeriya.

Sanatan ya ce dokar zata sa barayi, musamman ma'aikatan gwamnati su daina sata. A yadda ya ce, idan har aka yankewa wani ma'aikacin gwamnati a kasar nan hannu, dole kowa ya kiyaye.

Adeyemi ya sanar da niyyar nan tashi a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, a yayin tattaunawa da manema labarai a Lokoja, jihar Kogi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel