2027: Sule Lamido Ya Fadi Dalilin Goyon Bayan ADC duk da Yana Jam'iyyar PDP
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan matsayar da ya ɗauka ta goyon bayan jam'iyyar ADC
- Sule Lamido ya bayyana cewa ba zai taɓa ficewa daga PDP ba duk kuwa da goyon bayan da yake yi ga haɗakar ƴan adawa ta ADC
- Ya nuna cewa yana goyon bayan ADC ne domin ceto Najeriya daga halin da gwamnatin APC ta jefa ta a ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi magana kan goyon bayansa ga jam'iyyar ADC ta ƴan haɗaka.
Sule Lamido ya bayyana cewa ko da yake yana marawa jam’iyyar ADC baya, ba zai gushe ba wajen yin biyayya ga PDP.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Sule Lamido ya bayyana haka ne yayin wani taron tallafa wa jama'a da Sanata Mustapha Khabeeb a shirya a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan
ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Sule Lamido ke goyon bayan haɗaka?
Tsohon gwamnan, wanda ke cikin waɗanda suka assasa jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa haɗa kan jam’iyyun adawa an yi shi ne don ceto ƴan Najeriya daga mummunan mulkin APC da kuma sake gina ƙasar nan.
"Eh, ina goyon bayan haɗakar jam’iyyun adawa ƙarƙashin ADC, amma ya zama dole a sani cewa ba zan taɓa barin PDP ba."
"Na gina wannan gida da gumi da ƙwazo na. A yanzu aikina shi ne bayar da shawarwari da tabbatar da cewa Najeriya ta koma kan turbar da ta dace."
- Sule Lamido
Ya soki gwamnatin APC a matakin jiha da na ƙasa, yana mai cewa sun gaza a duk fannoni na mulki, rahoton Tribune ya tabbatar.
"Ƴan majalisar PDP daga Jigawa suna yi wa jama’a hidima. Ƴan majalisar APC kuma? Kansu kawai suke yi wa. A bari jama’a su yi hukunci."
- Sule Lamido

Source: Facebook
A wata alamar haɗin kai da goyon bayan jam’iyyun adawa a jihar, Sule ya gabatar da Kabiru Hussaini, shugaban jam’iyyar ADC na jihar, ga gungun magoya bayan PDP da ke wurin.
Sanatan Jigawa ya yi rabon tallafi
Sanata Mustapha Khabeeb, wanda ya shirya taron, ya jaddada ra’ayin tsohon gwamnan Lamido, inda ya tuna wa mahalarta taron tarihin ci gaban PDP, musamman a lokacin mulkin Sule Lamido a matsayin gwamna.
"Daga 1999 zuwa 2015, musamman ƙarƙashin Sule Lamido, Jigawa ta samu gaba, tituna, makarantu, asibitoci, da sauyi na gaskiya. Me muke da shi yanzu? APC ba ta kawo komai ba sai yunwa da rashin fata."
- Sanata Mustapha Khabeeb
Sanata Mustapha Khabeeb ya kuma bayyana irin ƙoƙarinsa na ci gaba da aikin PDP ta hanyar shirye-shiryen tallafawa al’umma da dama.
Sule Lamido ya shirya shiga haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa ya shirya shiga haɗaka don kifar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Sule Lamido ya nuna cewa a shirye yake ya shiga kowace irin haɗaka idan har za ta kai ga raba Tinubu da mulkin Najeriya.
Tsohon gwamnan ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƴan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
