Babachir Lawal: Tsohon Babban Jami'i a Gwamnatin Buhari Ya Fice daga APC

Babachir Lawal: Tsohon Babban Jami'i a Gwamnatin Buhari Ya Fice daga APC

  • Jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga manyan ƙusoshinta bayan ficewar tsohon sakataren gwamnatin tarayya a mulkin Muhammadu Buhari
  • Injiniya Babachir Lawal ya sanar da ficewarsa ne a hukumance daga jam'iyyar APC a cikin wata wasiƙa da ya rubuta
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana cewa yana dab da faɗin inda akalar siyasarsa za ta koma domin ganin cewa an inganta Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) a gwamnatin Muhammadu Buhari, Babachir Lawal, ya bar jam'iyyar APC.

Babachir Lawal ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC ne a hukumance.

Babachir Lawal ya fice daga APC
Babachir Lawal ya raba gari da jam'iyyar APC Hoto: Babachir Lawal
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa ficewar tasa na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya rubuta da kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babachir Lawal ya fice daga APC

Tsohon sakataren na gwamnatin tarayya ya aika da wasiƙar ne ga shugaban jam’iyyar APC na gundumar Banshika, da ke ƙaramar hukumar Hong a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da kwanan wata 29 ga watan Yuni, 2025, Babachir Lawal ya bayyana cewa ficewar tasa daga jam’iyyar za ta fara aiki nan take, ba tare da wani ɓata lokaci ba, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.

Babachir Lawal ya kuma yi nuni da cewa yana dab da bayyana sabuwar tafiyar siyasar da ya ɗauka, yana mai cewa zai fito fili da sabuwar jam’iyyar da zai haɗa kai da ita nan bada jimawa ba.

A cewar sa, wannan matakin da ya ɗauka na cikin wani shiri ne na haɗuwa da sauran ƴan ƙasa masu kishin ƙasa domin aiki tare wajen inganta Najeriya domin zama wuri mafi alheri ga kowa da kowa.

Hotunan Babachir sun fara yaɗuwa

A wani ɓangaren kuma, an fara yaɗa hotunan tsohon SGF ɗin a kafafen sada zumunta, inda aka gan shi tare da fitattun ƴan adawa.

Daga cikin waɗanda aka gan shi tare da su akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohuwar Sanata Binani Ahmed, wadda ta tsaya takarar gwamna a karkashin APC a zaben da ya gabata a jihar Adamawa.

Sauran kuma sun haɗa da tsofaffin sanatoci Ahmed Barata da Abdulazeez Nyako, da sauransu.

Kara karanta wannan

'Babu abin da zai raba ni da Buhari': Tsohon minista ya musanta barin jam'iyyar APC

Babachir Lawal ya fice daga APC a hukumance
Babachir Lawal ya rabu da jam'iyyar APC Hoto: @babachirlawal
Source: Twitter

Ana rade-radin cewa mutanen da ke cikin waɗannan hotuna su ne ke cikin haɗakar ƴan adawa ta ƙasa.

Babachir Lawal dai ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da ke sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu duk da cewa yana cikin jam'iyyar APC.

Kafin ficewarsa daga APC, an hango shi yana ɗasawa da jagororin haɗakar ƴan adawa masu son kifar da Tinubu a zaɓen 2027.

Babachir Lawal ya fallasa masu komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi wa ƴan siyasa masu komawa jam'iyyar APC tonon silili.

Babachir Lawal ya bayyana cewa ƴan siyasar da ke tururuwa suna komawa APC, suna yin hakan ne kawai don neman na abinci.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu ba kare muradun al'umma ba ne ya sanya su komawa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng