ADC: Buba Galadima Ya Fadi Dalilin Kwankwaso da NNPP na Kin Shiga Hadaka

ADC: Buba Galadima Ya Fadi Dalilin Kwankwaso da NNPP na Kin Shiga Hadaka

  • Jam’iyyar NNPP ta ce ba ta shiga haɗakar ADC ba ne domin guje wa barin nasu ginshikin su koma karkashin wata sabuwar kafa
  • Jigo a jam'iyyar, Buba Galadima ya ce babu hikimar barin NNPP domin bin wasu da ba su zo shiga jam’iyyarsu ba
  • Yana ganin kowanne ɗan siyasa ya kafa tasa jam’iyyar kamar yadda Rabiu Kwankwaso ya yi, domin gwada ƙarfinsa a siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa babban dalilin da ya sa ba ta shiga kawancen jam’iyyar ADC ba shi ne domin kauce wa sake-reshe-kama-ganye a siyasa.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan adawar Najeriya ke hada kai domin tunkarar APC da Bola Tinubu a zaben 2027.

Buba Galadima ya ce ba za su shiga hadaka ba
Buba Galadima ya ce ba za su shiga hadaka ba. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Sakataren kwamitin amintattu na NNPP kuma jigo a siyasar Najeriya, Buba Galadima, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da BBC Hausa a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ba za mu bar NNPP ba' – Buba Galadima

Buba Galadima ya ce jam’iyyar ADC da shugabannin kawancen sun ki shiga NNPP, amma suna son a bar jam’iyyar Rabiu Kwankwaso a rungumi tasu.

A hirar da ya yi, Buba Galadima ya bayyana hakan a matsayin rashin tabbas da rashin dacewa a siyasa.

“Su ba su zo suka shiga tamu jam’iyyar ba, sai kawai mu bar tamu mu shiga tasu a wane dalili?”

-Inji Buba Galadima cikin rashin gamsuwa da tsarin hadakar.

Ya kuma kalubalanci duk wani ɗan siyasa da ke da muradin canji da ya kafa tasa jam’iyya kamar yadda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi, domin gwada ƙarfinsa.

Wadanda suka shiga hadakar ADC

Bayanin Buba Galadima na zuwa ne bayan manyan ‘yan adawa biyu, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun goyi bayan hadaka a ADC domin su fuskanci Bola Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya rasa tikitin takarar shugaban ƙasa na NNPP a 2027, an faɗi dalili

Rahotanni sun bayyana cewa wasu tsofaffin manyan jam’iyyar APC ma suna goyon bayan sabon kawancen domin su kwace tsarin mulki a 2027.

Sai dai har yanzu jam’iyyar NNPP da jagoranta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba su shiga kawancen ba, lamarin da ke nuna akwai bambanci a dabarun siyasa.

Buba Galadima ya ce hadaka na da kyau

Duk da wannan bayani, Buba Galadima ya bayyana cewa kafa haɗakar ADC wani abu ne da zai iya ƙarfafa gwiwar jam’iyyun adawa da kuma jawo hankalin masu son sauyi a Najeriya.

Sai dai ya ce tsarin haɗakar na da jan aiki a gabansa saboda rashin ƙayyadadden tsari da jagoranci wanda zai iya janyo rarrabuwar kai.

'Yar Buba Galadima ta ba Tinubu shawara

A wani rahoton, kun ji cewa Zainab Buba Galadima ya ta ce lallai akwai jan aiki a gaban shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Zainab Buba Galadima ta ce jama'a da dama a Arewacin Najeriya ba za su zabi Bola Tinubu ba a bisa hasashen da ta yi.

Baya ga haka, ta ce masu hadaka a ADC za su kara zama barazana ga Bola Tinubu tana mai ba APC shawarin cewa su farka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng