Yadda Jagororin APC Suka Ki Tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje Ya Yi Murabus

Yadda Jagororin APC Suka Ki Tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje Ya Yi Murabus

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata a jihar Kano
  • Daya daga cikin abubuwan da suka na hankali shi ne rashin ganin jagororin APC ko magoya baya an tarbe shi yayin ziyarar
  • Tuni aka fara hasashe, ana danganta lamarin da sabanin siyasa musamman bayan Abdullahi Ganduje ya bar shugabancin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ba a ga shugabannin APC na Kano sun tarbi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a ziyarar da ya kai wa iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata.

Yayin da jami’an gwamnatin Kano daga jam’iyyar NNPP suka karɓi Shettima yadda ya kamata, ba a ga wani jigo daga cikin shugabannin APC na jihar a wajen taron ba.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima
Ana hasashen akwai baraka a APC Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan lamari ya jawo tambayoyi da hasashe, inda wasu ke ganin cewa hakan na nuna akwai rabuwar kai a jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kuma na zuwa ne bayan saukar da Dr Abdullahi Umar Ganduje daga kujerar shugabancin jam’iyyar a ƙasa da abubuwan da suka zo kafin wannan.

Babu jagororin APC a tarbar Kashim Shettima

Gidan rediyon Freedom Radio ya wallafa a shafinsa na Facebook tambayar neman inda shugabannin APC na Kano suka shiga yayin da NNPP ke tarbar Kashim.

Shettima ya kai ziyarar ne domin ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata, ɗan kasuwa kuma mai taimakon al’umma da ya kusa shekaru 100 a raye.

Rahoton ya kara da cewa a irin wannan muhimmin taro, al’ada ce manyan ’yan jam’iyya da magoya bayansu su fito su tarbi manyan jami’an gwamnati, musamman mataimakin shugaban ƙasa.

Ana hasashen baraka a jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Yaƴan jagororin ADC da ke cikin jam'iyyun APC da PDP a yau

Rashin yiwa Kashim Shettima da manyan APC suka yi na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bar shugabancin jam'iyya.

Wannan sauyi ya faru ne sakamakon shirye-shiryen siyasa da dabaru da ke faruwa a jam’iyyar domin fuskantar zaɓen 2027.

Kashim Shettima yayin ta'aziyya ga iyalan Dantata
Babu manyan APC a tarbar Kashim a Kano Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Wannan sauyi ya faru ne sakamakon shirye-shiryen siyasa da ake gudanarwa gabanin zaben 2027, kuma makonni bayan takaddama a kan kalaman Ganduje a Gombe.

Masana sun bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin APC na Kano ba su ji daɗin yadda Ganduje ya sauka daga shugabanci ba, kuma suna zargin akwai rawar da Shettima.

APC ta yi martani kan rashin tarbar Kashim

Sakataren APC a Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya musanta jita-jitar cewa rashin halartar shugabannin jam’iyyar alama ce ta baraka a cikin gida, yana mai cewa ba komai bane illa kuskuren sadarwa.

A kalamansa:

“Mun san da zuwan nasa, amma bayanin ya zo a makare. Kafin mu yi shiri da tura mutane, lokaci ya kure. Tun da gwamnati ta kusa da shi kuma ta riga ta shirya, sai ta ɗauki nauyin tarbar.”

Kara karanta wannan

ADC: Bayan hasashen El-Rufa'i, sabon rikici ya danno jam'iyyar hadakar adawa

“Gaskiya wannan ba ya da alaka da wata baraka. Mun samu bayanin ne a makare, hatta gwamnatin jiha ma haka ta samu. Daga baya mun aike masa da godiya bisa ziyarar, kuma ya fahimta matuƙa.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Dr Musa Auwal, wani masanin kimiyyar siyasa, ya ce jam’iyyar APC na bukatar taka tsantsan.

A cewarsa:

“Idan manyan shugabanni suka fito a bainar jama’a da rarrabuwar kai, hakan na raunana su tare da ƙarfafa ’yan adawa.”

Matsalar APC da Ganduje, Shettima

Saukar da Dr Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa ya sanya gurguncewa a tsari da haɗin kai tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, musamman a jihar Kano.

Wannan lamari ya kasance wata alama ce ta rikice-rikicen cikin gida da ake ta kokarin ɓoye wa idon jama’a.

Rikicin da ya biyo bayan saukar Ganduje ya haifar da rashin tabbas, inda wasu magoya baya da shugabanni ke jin an yi masa rashin adalci – lamarin da ya haifar da fushi da kin nuna goyon baya ga wasu manyan gwamnati kamar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Kashim Shettima ya ziyarci garin Kano

A baya, mun wallafa cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata a Kano.

Kara karanta wannan

Saukar Ganduje daga shugabancin APC ya bar babban giɓi a APC, an sa ranar taron NEC

Daga cikin shawarwarin da ya bayar ga iyalan, ya bukaci su zauna lafiya cikin haɗin kai da fahimtar juna, musamman a lokacin da ake fuskantar batun rabon gado.

Ya nemi iyalan marigayin su ci gaba da ɗaukar halayen da suka bayyana rayuwarsa, musamman na gaskiya, taimakon al’umma da kyakkyawar zuciya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng