ADC: Bayan Hasashen El Rufa'i, Sabon Rikici Ya Danno Jam'iyyar Hadakar Adawa
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu, ya yi fatali da yadda yan adawa suka shiga cikinta
- 'Dan siyasar ya yi zargin cewa sun shiga ADC ta barauniyar hanya ganin cewa wa'adin Ralph Nwosu ya kare kusan shekaru uku baya
- Kachikwu ya nanata cewa babu wanda zai shigo masu jam'iyya ta hanyar da ba ta dace ba, sannan su aminta a yi tafiya tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu, ya nesanta kansa daga sabon jagorancin jam’iyyar da aka ƙaddamar a ranar Laraba.
Ya kara da bayyana cewa karɓar jam’iyyar da wasu gungun ‘yan adawa suka yi haramtaccen mataki ne da ta nuna tsantsar rashin da’a.

Kara karanta wannan
ADC: Haɗakar Atiku ta fara ƙarfi, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

Source: Twitter
Channels ta ruwaito Kachikwu ya soki sabuwar haɗakar, yana zargin cewa sun shiga kawance da shugabancin jam’iyyar ADC na bogi kuma maras inganci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikici ya kunno cikin jam'iyyar ADC
Jaridar Daily Trust ta ce a cewar Kachikwu, wa’adin shugabancin Ralph Nwosu a matsayin shugaban jam’iyyar ADC ya ƙare tun ranar 21 ga watan Agusta, 2022.
Ya ce sai dai har yanzu yana ci gaba da kiran kansa shugaban jam’iyyar, wanda hakan ya haifar da shari’o’i a kotuna daban-daban a fadin ƙasar.
A kalamansa:
“Za ka iya gina wani abu a kan iska? Za ka iya aske wa mutum kai alhali ba ya nan? Za ka iya shiga gidan mutum ta bayan fage ka ce kai ne mai gidan?
“Wadannan mutanen da suka fito daga tsohon lokaci mai baƙin tarihi a siyasar Najeriya sun shiga matsala ta hannun mutumin da ya jawo matsala a tarihin ADC.”
Tsohon dan takarar ADC ya dauki zafi
Kachikwu ya bayyana yan haɗakar adawa a matsayin wasu da masu neman wata kafa domin ci gaba da wawashe dukiyar ƙasa.

Source: Facebook
A cewarsa, wannan lamari ya ƙara jaddada rashin gamsuwa da yadda jam’iyyun siyasa ke tafiya a Najeriya, yana mai cewa:
“Suna da’awar suna yaƙi don kare hakkin talakawa kuma suna cewa suna kokarin ceto ƙasa. Amma abin da ke ruɗar da ‘yan Najeriya shi ne, waɗannan mutanen – waɗanda suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, tsofaffin gwamnoni, ministoci da masu mukaman siyasa – sune suka shugabanci al’amuran wannan ƙasa sama da shekaru arba’in.”
Ya yi zargin cewa, duk tsawon shekaru da suka shugabanci ƙasa, Najeriya ba ta da abin nunawa sai rabuwar kai ta ƙabilanci da addini da jawo matsaloli a fadin kasa.
El-Rufa'i ya yi magana kan rikici a ADC
A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa sun amince da amfani da ADC a matsayin dandalin wucin gadi yayin da ake son kafa sabuwar jam’iyya.
El-Rufa’i ya ce haɗin gwiwar da suka yi da ADC na ɗan lokaci ne saboda ita ce jam’iyyar da ba ta da matsaloli da yawa idan aka kwatanta da wasu jam’iyyun kasar nan.
Tsohon gwamnan ya zargi gwamnati mai ci da katsalandan cikin ƙoƙarin da ‘yan adawa ke yi na kafa sabuwar jam’iyya., inda ya ce kar a yi mamaki idan aka ji rigima a SDP.
Asali: Legit.ng
