ADC: Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Fice daga PDP a jihar Kano

ADC: Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Fice daga PDP a jihar Kano

  • Wani jigo a PDP reshen a jihar Kano, Ibrahim Ali Amin Little, ya sanar da ficewa daga cikinta bisa dalilai na rikicin shugabanci
  • Ali Amin Little, Wanda tsohon dan takarar gwamna ne a jihar ya kuma yi zargin cewa an daina mutunta dimokuraɗiyyar a PDP
  • A cikin wata wasika da ya aika ga shugaban jam'iyyar a mazabarsa, ya shaida cewa yanzu ya nufi jam'iyyar hadakar yan adawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon dan takarar gwamnan Kano, kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP, Ibrahim Ali Amin Little ya ce daga yanzu, ya bar jam'iyyar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya aika zuwa ga shugaban PDP na Tudun Wada, awanni kadan da bayyana SDP a matsayin jam'iyya adawa da sake zaben APC.

Kara karanta wannan

'Gaba ta kai mu,' Ministan Tinubu ya hango amfanin da ADC za ta yiwa APC a 2027

Ali Amin Little ya koma ADC
Tsohon dan takarar gwamna ya bar PDP a Kano Hoto: Abubakar Lamido/AbdulRasheeth Shehu
Source: Facebook

Wasikar, wacce Adnan Mukhtar Tudun Wada ya wallafa a shafinsa na Facebook ta kuma bayyana dalilansa na hakura da PDP da kuma sabuwar hanyar da zai bi a siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al Amin Little ya bar jam'iyyar PDP

A wasikar, Ibrahim Ali Amin ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda halin da jam’iyyar ke ciki a matakin jiha da na ƙasa.

A kalamansa:

“Na kasance ɗan PDP mai ƙaunar jam’iyya kuma mai riƙon katin zama cikakken danta daga mazabar Tudun Wada. Na ba da gudunmawa a lokuta da dama wajen ci gaban jam’iyyar."

Ya bayyana damuwarsa da halin rikice-rikicen shugabanci da ya addabi jam’iyyar, yana mai cewa hakan ya haifar masu da illa matuka.

“Rikicin shugabanci ya rusa tubalin haɗin kai da ake buƙata domin cigaban jam’iyya. Rashin mutunta dimokuraɗiyyar cikin gida da kaucewa ƙa’idojn da aka gina jam’iyyar a kansu ya sanya ba zan iya cigaba da kasancewa cikin PDP da kyakkyawar niyya ba."

Kara karanta wannan

Plateau: Yayin da ake watsewa Tinubu, hadimin gwamna ya ajiye aiki, ya dawo APC

Mataki na gaba bayan barin PDP

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya shaidawa Legit ta kafar WhatsApp cewa zai shiga jam'iyyar hadakar adawa domin a kara matsa lamba wajen ceto Najeriya.

A cewarsa:

“Na yanke shawarar ficewa daga PDP tare da shiga haɗakar siyasa da ke da nufin ceto ƙasar nan da dawo da ainihin dimokuraɗiyya.”
Jagororin ADC na kasa
Ali Amin Little ya ce ADC za ta zama mafita Hoto: AbdulRasheeth Shehu
Source: Facebook

Ya kara da cewa a yanzu, abin da aka saka a gaba shi ne a sake fasalta ADC, yadda za ta samu nasarar karawa da APC kafada da kafada a babban zabe mai zuwa.

Ibrahim Ali Amin Little ya ce:

"A yanzu, ana ƙoƙarin gina jam'iyya ne domin ba ta damar bugawa da APC a zaben gaba."

ADC: An bayyana jagoran jam'iyyar adawa

A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, ya shirya jagorantar sabon gungun haɗakar ‘yan adawa gabanin zaben 2027.

Wannan na ƙunshe ne a cikin jawabin da Ralph Nwosu, wanda ya kafa kuma ya kasance shugaban farko na ADC ya gabatar a taron da sabuwar haɗakar a Abuja.

Tun da farko, ƙungiyar ta naɗa David Mark a matsayin shugaban riko, tare da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakataren rikon ƙwarya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng