Ta Faru Ta Kare: Kakakin Majalisar Dokoki Ya Yi Murabus a Filato, An Zabi Sabo
- Kakakin Majalisar Filato, Hon. Gabriel Dewan, ya yi murabus, inda aka zaɓi Nanloong Daniel na APC a matsayin sabon shugaba ba tare da hamayya ba
- Murabus ɗin Dewan ya biyo bayan taron sirri da Gwamna Caleb Mutfwang don warware rikicin shugabanci da rashin daidaiton siyasa a jihar
- An sa ran jagorancin Rt. Hon. Daniel zai dawo da zaman lafiya da ci gaba ga majalisar Filato, tare da haɗin gwiwa tsakanin bangarorin gwamnati
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - A wani mataki mai ban mamaki, Hon. Gabriel Dewan, kakakin majalisar dokoki na jihar Filato ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Laraba.
'Yan majalisar, sun zabi Hon. Nanloong Daniel, mai wakiltar mazabar Mikang, a matsayin sabon shugaban majalisar domin maye gurbin Dewan.

Source: Facebook
An zabi sabon shugaban majalisar Filato
Zaɓen ya gudana ne yayin wani zama na gaggawa da aka yi a dakin taron majalisar na wucin gadi da ke tsohuwar fadar gwamnati a Jos, a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Nanloong Daniel, ɗan jam’iyyar APC, ya rike mukamin shugaban masu rinjiye a majalisa ta tara, wanda ya sa ake ganin zai nuna gogewa a sabon mukaminsa.
'Yan majalisar Filato 24 ne suka zaɓi Daniel ba tare da adawa ba, wanda ake ganin zai dawo da zaman lafiya a majalisar bayan rikici na dogon lokaci da aka yi.
Tasirin murabus din Gabriel Dewan a majalisa
An rahoto cewa Gabriel Dewan, wanda shi kaɗai ne ɗan jam’iyyar YPP a majalisar, ya yi murabus ne a wani mataki na warware rashin jituwar da ake fama da ita a majalisar.
Sauyin shugabancin ya biyo bayan wata ganawa ta bayan fage tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang, Dewan da wasu ‘yan majalisa domin shawo kan rikicin shugabanci a jihar.
Murabus ɗin Dewan ya samo asali ne daga rashin daidaito na tsarin raba madafun iko, ganin cewa shi da Gwamna Mutfwang dukkansu sun fito daga yankin Filato ta Tsakiya.
Masana harkokin siyasa sun bayyana zaɓen Daniel a matsayin mataki na wanzar da zaman lafiya bayan rikicin da ya dabaibaye majalisar tun bayan sauke ‘yan majalisar PDP.

Source: Facebook
Yadda aka zabi sabon kakakin majalisar Filato
Bayan wannan zaman, an ce mataimakin shugaban majalisar, Hon. Gwotta Ajang ya jagoranci zaman na gaggawa, wanda ya tabbatar da mika mulki daga Dewan zuwa Daniel cikin lumana.
Hon. Naanbol Listick, mai wakiltar Langtang ta Arewa ta Tsakiya ne ya gabatar da sunan Daniel, sannan Hon. Abdul Yanga daga mazabar Mangu ta Arewa maso Gabas ya mara masa baya.
Bayan zaɓen, Gwamna Mutfwang ya gana da sabon shugaban majalisar, inda ya bukace shi da ya karfafa haɗin gwiwa da bangaren zartarwa, inji rahoton SilverBird TV.
Ana sa ran shugabancin Daniel zai kawo sabon salo na kwanciyar hankali da cigaba a majalisar jihar Filato yayin da ake ci gaba da daidaita siyasar jihar.
APC ta bukaci a tsige kakakin majalisar Filato
Tun da fari, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta yi barazanar gurfanar da kakakin majalisar Filato gaban kuliya kan kin rantsar da mambobinta 16.

Kara karanta wannan
ADC: Haɗakar Atiku ta fara ƙarfi, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya fice daga PDP
APC ta yi wannan barazanar ne bayan da kotun daukaka kara ta tabbatar da sahihancin 'yan majalisar na ta, amma Hon. Gabriel Dewan ya yi biris da hukuncin.
Shugaban jam'iyyar APC, Hon. Rufus Bature ya nuna damuwa kan matakin na kakakin Majalisar inda ya ce ya raina hukuncin kotu ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
