Jam'iyyar APC Ta Yi Sababbin Ƴan Majalisa 9 a Jihar Arewa, Sun Karbi Rantsuwar Kama Aiki

Jam'iyyar APC Ta Yi Sababbin Ƴan Majalisa 9 a Jihar Arewa, Sun Karbi Rantsuwar Kama Aiki

  • A karshe, shugaban majalisa dokokin jihar Filato, Gabriel Dewan, ya rantsar da ƴan majalisa 9 cikin 16 na jam'iyyar APC
  • Mambobin majalisar waɗanda kotu ta bai wa nasara sun karɓi rantsuwar kama aikin ne ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 a Jos
  • Rt. Hon. Dewan ya bayyana cewa ya dogara da wata takarda da aka aiko masa wajen rantsar da sababbin ƴan majalisar dokokin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Filato - Shugaban majalisar dokokin jihar Filato, Gabriel Dewan, ya rantsar da 9 daga cikin ƴan majalisa 16 na jam'iyyar APC.

An tattaro cewa shugaban majalisar ya bai wa sababbin mambobi tara rantsuwar kama aiki ne da safiyar ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 a Jos, babban birnin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen bincike a babban banki CBN, ya ɗauki mataki

Kakakin majalisar Filato, Gabriel Dewan.
Yan majalisa 9 cikin 16 na APC sun karbi rantsuwar fara aiki a Filato Hoto: Hon. Gabriel Dewan
Asali: Facebook

Kamar yadda jariar The Nation ta ruwaito, majalisar ta kuma naɗa mamba mai wakiltar mazaɓar Jos ta Gabas a matsayin mataimakin kakakin majalisar dokokin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honorabul Dewan ya bayyana cewa ya amince da rantsar da ƴan majalisar ne bayan wata wasiƙa da aka turo masa.

Yadda aka yi rigima kan kujerun majalisa

Idan baku manta ba, kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta kori ƴan majalisa 16 da suka lashe zaben karkashin inuwar PDP kana ta ayyana ƴan takarar APC a matsayin sahihan waɗanda suka ci zaɓe.

Kotun ta ɗauki wannan mataki ne bisa hujjar cewa jam'iyyar PDP ba ta da halastaccen tsarin da za ta iya tsayar da ɗan takara a jihar Filato saboda saɓawa doka.

Sai duk da kotu ta tsige su, ƴan majalisun PDP 16 sun yi kira ga kotun kolin Najeriya ta duba hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuma ta masu adalci.

Kara karanta wannan

Miyagu sun farmaki ɗan majalisar tarayya a jihar Arewa yayin da ya halarci taro a mazaɓarsa

Bayan haka kuma ranar 23 ga watan Janairu, mambobin PDP suka lashi takobin cewa za su ci gaba da halartar zaman majalisa, rahoton Leardership.

Tinubu zai yi tazarce a 2027

A wani rahoton kuma Yekini Nabena na da ra'ayin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu sai ya yi shekara takwas kan karagar mulkin Najeriya.

Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labaran na jam'iyyar APC ya yi nuni da cewa duk wasu ƙulle-ƙullen da ƴan adawa suke yi ba zai yi tasiri ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel