Filato: Ƴan Majalisa 16 Na Arewa da Suka Samu Nasara a Kotun Ɗaukaka Kara Sun Shiga Matsala

Filato: Ƴan Majalisa 16 Na Arewa da Suka Samu Nasara a Kotun Ɗaukaka Kara Sun Shiga Matsala

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Filato ya yi magana kan rantsar da ƴan majalisar APC 16 da suka samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara
  • Gabriel Dewan ya ce ba zai karɓe su ba kuma ba zai yarda korarrun mambobin PDP su sake dawowa majalisar ba
  • A cewarsa yana da umarnin kotu na hana rantsar da ƴan majalisar, inda ya ce a yanzu zasu ci gaba da zama su takwas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Shugaban majalisar dokokin Filato ya ce ba zai rantsar da ‘yan majalisa 16 da kotun daukaka kara ta ayyana a matsayin wadanda suka lashe zabe a mazabunsu ba.

Tun farko dai kotun ɗaukaka ƙara ta tsige mambobi 16 na jam'iyyar PDP kana ta bai wa ƴan takarar APC nasara a zaben 18 ga watan Maris, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Abu 1 da ya sa aka tsige shugaban majalisar dokokin jihar APC daga muƙaminsa

Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau.
Filato: Ƴan Majalisa 16 Na Arewa da Suka Samu Nasara a Kotun Ɗaukaka Kara Sun Shiga Matsala Hoto: Hon. Gabriel Dewan Kudangbena
Asali: Facebook

Yan majalisar APC 16 sun gamu da cikas

Amma da yake tsokaci bayan majalisar ta dawo daga hutu, shugaban majalisar dokokin Filato, Gabriel Dewan, ya ce ba zai baiwa waɗanda suka samu nasara a kotu rantsuwar kama aiki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dewan ya ƙara da cewa yana da umarnin kotu a hannu wanda ya dakatar da shi daga aminta da ƴan majalisar na APC a matsayin mambobin majalisar Filato.

Ya kuma ce ba zai karɓi korarrun mambobin PDP 16 da suka yi yunkurin komawa zaman majalisar a ranar Talata ba duk da cewa kotun zaɓe da kotun daukaka kara sun kore su.

Wane hali majalisar dokokin Filato zata shiga?

Sai dai kakakin majalisar ya ce shi da sauran yan majalisa 8 zasu ci gaba da ayyukan majalisa yayin da korarrun na PDP 16 da na APC zasu jira na wani lokaci a yanzu.

Kara karanta wannan

Mahara sun shiga jami'ar BUK Kano sun yi garkuwa da ɗalibai? Gaskiya ta bayyana

Dewan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Jos, biyo bayan dawowa daga dogon hutun da ‘yan majalisar suka yi.

An yi dirama a zauren da majalisar ke zama na wucin gadi da ke tsohon gidan gwamnati ranar Talata, yayin da korarrun ƴan majalisa 16 na PDP suka so koma wa majalisar.

Yan sanda dai sun tsaurara tsaro a wurin, wanda sai da ta kai ga suka harba wa yan majalisar barkono mai sanya hawaye, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Abinda ya jawo wa kakakin majalisar Ogun matsala

A wani rahoton na daban Ɗan majalisa ya bayyana asalin dalilin da ya sa aka tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo.

Ranar Talata, 22 ga watan Janairu, ƴan majalisa 18 cikin 26 suka tsige kakakin majalisar bisa zargin almubazzaranci da kuɗinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel